Da Dumi-Dumi: Mutane sun mutu yayin da gini ya ruftawa masu ibada ana tsaka da bautar Allah
- Wani sabon ginin Coci a jihar Delta da aka fara shiga yau, ya kife kan mutane da yawa da yammacin Talata yayin da suke tsaka da Ibada
- Rahoto ya tabbatar da cewa zuwa yanzun an gano gawarwakin mutum 10, kuma an zaro wasu mutum takwas ba su ji rauni ba, wasu hudu kuma suna Asibiti
- Tuni jami'an bada agajin gaggawa na Red Cross, jami'an hukumar kashe gobara da wasu jiga-jigan gwamnatin jihar Delta suka dira wurin
Delta - Ginin cocin Housing Salvation dake Okpanam, karamar hukumar Oshimili ta arewa a jihar Delta, ya kife kan mutane suna cikin ibadar Allah.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har yanzun ba'a gano adadin yawan mutanen da Cocin ta danne ba, amma an zaro gawarwakin aƙalla mutum 10.
Ginin cocin, wanda rahotanni suka tabbatar da yau ne karo na farko da aka fara amfani da shi, ya rushe ne da misalin ƙarfe 5:55 na yammacin ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin ceto sun zaro mutum takwas da ba su ji rauni ba, yayin da aka gaggauta kai wasu mutum hudu asibitin Asaba Special.
Wane mataki hukumomi suka dauka?
Sakataren fadar gwamnatin jihar Delta, Chief Patrick Ukah, kwamishinan lafiya, Dakta Ononye Mordi, sun dura wurin da lamarin ya faru.
A yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, jami'an agaji na Red Cross da Jami'an kwana-kwana sun isa wurin domin cigaba da aikin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.
The Nation ta rahoto cewa Mabiyan coci, da iyalan waɗan da lamarin ya rutsa da su, da masu jajantawa sun shiga matukar damuwa har da zubda hawaye, suna kokarin nemo yan uwansu.
Matasan yankin, jami'an kashe gobara da jami'an yan sanda sun haɗa kai wajen kokarin fitar da mutanen da ginin ya danne.
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga
Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.
PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.
Asali: Legit.ng