Yanzu-Yanzu: An tsinci gawar babban ma'aikacin man fetur bayan iyalansa sun biya N5m ga masu garkuwa
- Yan bindiga da suka yi garkuwa da Mr Ojonimi Ossai, ma'aikacin kamfanin man fetur na Shell sun halaka shi
- Hakan na zuwa ne bayan yan uwansa sun biya kudin fansa na Naira miliyan 5 da masu garkuwan suka bukata
- Masu garkuwan sun sace Ossai ne a hanyarsa na zuwa jana'izar surukinsa a jihar Kogi duk da cewa da farko bai yi niyyar zuwa ba
Jihar Kogi - Masu garkuwa da suka sace Mr Ojonimi Ossai, ma'aikacin kamfanin man fetur na Shell sun halaka shi, Daily Trust ta ruwaito.
Sun halaka Ossai duk da cewa iyalansa sun biya Naira miliyan 5 da aka bukata matsayin kudin fansa.
Daily Trust ta rahoto cewa marigayi Ojonimi Ossai yana hanyarsa na zuwa halartar jana'izar surukinsa ne a karamar hukumar Mela/Odolu a karamar hukumar Kogi a lokacin da masu garkuwan suka kama shi a karshen makon da ta gabata.
Yan uwansa sun tabbatar da mutuwarsa
Wani majiya daga yan uwansa ya bayyana cewa an biya masu garkuwa N5m da suka bukaa, amma duk da haka aka gano gawarsa a daji a ranar Talata.
Marigayi Ossai, wanda ya shafe shekaru 23 yana aiki da kamfanin Shell, bai so zuwa jana'izar ba amma yan uwansa suka matsa masa ya bar gidansa da ke PortHarcourt.
"Ya zo gida a wata tsohuwar mota domin bata kama saboda masu garkuwa, amma duk da haka ya fada hannunsu a hanyar Itobe-Anyigba. Mun dako gawarsa a daji da safe," in ji wani dan uwansa.
Abin da yan sanda suka ce
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar, William Aya, ya ce bai riga ya samu bayani game da afkuwar lamarin ba.
Bara, a irin wannan lokacin, an bindige wani ma'aikacin man fetur mazaunin Saudiyya, Ogacheku Atanu, a yayin da ya tafi hutu a Idah.
Ku saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng