Kano: Kasuwar 'yan achaba ta bude, suna karakaina a tituna yayin yajin aikin 'yan sahu
- Masu babura wadanda aka fi sani da 'yan achaba sun mamaye titunan jihar Kano sakamakon fadawa yajin aikin matukan adaidaita sahu
- A ranar Litinin ne matukan adaidaita sahu na jihar Kano suka fada yajin aikin kan yawan kudin da gwamnati ke karba a hannunsu na rijista
- Sai dai ba rashin ababen hawan kadai ke damunsu ba, sun nuna damuwarsu gudun fadawar jama'a harkokin garkuwa da mutane da sata
Kano - A rana ta biyu bayan masu Napep, wadanda aka fi sani da 'yan adaidaita sahu suka fada yajin aiki a Kano, masu babura ne suka cika tituna yayin da mutane suke neman ababen hawa.
Yajin aikin ya dakile kai komo a Kano ranar Litinin, wanda ya tilasta mutane da dama, wadanda suka hada da dalibai da kuma 'yan kasuwa zaman gida dalilin rashin ababen hawan da zai kai su makarantu da wuraren aiki.
Daily Trust ta ruwaito yadda sabon yajin aiki a birnin ya zama karo na biyu a cikin shekara 1.

Asali: UGC
Matukan suna yajin aikin ne saboda karin kudin rijistar da hukamar kula da al'amuran tituna (KAROTA) ta kara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar a yanzu tana amsar N18,000 a matsayin kudin rijista ga sabbin matuka, yayin da take amsar N8,000 duk shekara daga masu adaidaitan.
Matukan, wadanda suka ki amincewa da hakan, sun ki fitowa aiki a safiyar ranar Litinin har zuwa ranar talata.
Bayan amfani da babura a matsayin keke Napep, kananan motoci da motocin gida ne ake amfani da su domin kai komo, wanda hakan ne ya zama abin firgici ga al'umma game da harkar tsaro da garkuwa da mutane.
Yayin maida martani a ranar farko game da yajin aikin, shugaban hukumar kula da tituna, KAROTA, Baffa Babba Danagundi, ya ce gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai dan ganin karshen yajin aikin.

Kara karanta wannan
Jami’ar Kano Ta Ɗage Yin Jarrabawa Saboda Yajin Aikin Masu Baburan A-Daidaita-Sahu
"Gwamnatin tana kokarin nemo wata hanya saboda ta na ganin ta yi sakacin barin abun hawa iri gudu da zai dunga kai komo a jihar yanzu."
Sai dai shugaban kungiyar matuka 'yan sahu, Sani Sa'idu Dankoli, ya ce matakin da suka dauka bai zo a ba-zata ba saboda sun sanar tun sati 2 kafin nan, Daily Trust ta ruwaito.
Amma ya tabbatar da cewa za su sulhunta kuma matukan adaidaitan za su dawo kan tituna a rana ta biyu.
"Muna tattaunawa da mutanenmu dan janye yajin aikin saboda yawancinmu ba mu da abinda za mu ci da iyalanmu, idan ba mu fito mun nema kullum ba. Saboda haka, yajin aikin ya shafi kowa. Muna tabbatar muku a rana ta biyu, zamu dawo kan aikinmu."
Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki
A wani labari na daban, Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu a cikin shekara 1 da matukan adaidaitan suka tsaida amfani da ita wanda ya janyo ci baya ga tattalin arzirki da walwalar mazauna jihar.
An kiyasta cewa, yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin ya janyo a kalla asarar naira miliyan 6 wanda jihar ke samun harajin kowacce rana naira 100 ga kowanne mutukin adaidaita a jihar.
A bangaren matukan adaidaitan kuwa, sun tafka asarar akalla kimanin N300,000,000, Daily Trust ta ambata wanda tace suna samun tsakanin N5,000 da N7000 a kowacce rana.
Asali: Legit.ng