Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

  • Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Cif Ernest Shonekan ya riga mu gidan gaskiya, inji rahotanni daga majiyoyi
  • Rahoto ya ce ya rasu ne a jihar Legas, inda ya kai shekaru 85 a duniya kafin ya koma ga mahaliccinsa
  • Shonekan shi ne shugaban rikon kwarya da ya gaji mulkin janar Badamasi Babangida a shekarar 1993

Legas - Cif Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya wacce ta gaji mulkin Janar Ibrahim Babangida, ya rasu.

Shonekan ya rasu a jihar Legas yana da shekaru 85 a duniya, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Ya kasance shugaban kasa Najeriya na wucin gadi tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba, 1993 lokacin da aka hambarar da shi a juyin mulkin da marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata

Shoken ya rasu
Da dumi-dumi: Tsohon shugaban Najeriya Ernest Shonekan ya rasu | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, Shonekan wanda danginsa ya fito ne daga Abeokuta ta Jihar Ogun, an haife shi kuma ya girma a Legas.

Ya yi karatu a Makarantar Grammar C.M.S da Kwalejin Igbobi da ke Legas, kafin ya yi digirin digirgir a Jami’ar Landan, inda daga baya aka tabbatar dashi a matsayin lauya.

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talata

Allah ya yiwa Sheikh Yahaya Usman Gidadawa rasuwa a safiyar talatar nan, Farfesa Mansur Sokoto ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

Marigayin ya kasance mai jawa Farfesa Mansur Sokoto bakin littafin Sahihul Bukhari.

Ya kara da cewa za'a yi masa Sallar Jana'iza karfe 12 na rana a yau Talata, 11 ga Junairu, 2022 a cikin garin sokoto.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

Kungiyar Izala a sakon ta'aziyyarta ta bayyana cewa Marigayin ya rasu bayan fama da jinya.

Ya rasu ya bar mata 4 da yara 40.

A wani labarin, mutuwa ta sake sallama a gidan marigayi Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi a jihar Kwara.

Oba Oyewumi ya rasu ne a ranar 12 ga watan Disamba yana da shekaru 95, inda aka tattaro cewa diyar marigayi sarkin, Farfesa Taibat Danmole ta rasu a ranar Asabar 8 ga watan Janairu tana da shekaru 71 a duniya.

Wasu majiyoyi a fadar sun shaida wa jaridar Punch a ranar Lahadi cewa Danmole ta dade tana jinya kafin ta rasu ranar Asabar, kwanaki 28 bayan da mahaifinta ya yi sallama da duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: