Sunaye da yanki: Bayan luguden Super Tucano, ƴan ISWAP sun sauya shugabanni

Sunaye da yanki: Bayan luguden Super Tucano, ƴan ISWAP sun sauya shugabanni

  • Bayan luguden wutan da Super Tucano ya yi wa mayakan ta'addanci da shugabannin ISWAP a Borno, sun yi taron kwana biyu a Borno inda suka sauya shugabanni
  • Kamar yadda majiya mai karfi ta tabbatar, 'yan ta'addan sun samu shugabancin Sani Shuwaram yayin taron inda kwamitin Shura da manyan kwamandoji suka bayyana
  • Cikin yankunan da aka sauyawa kwamandoji akwai, Garal, Kayowa, Tumbum Murhu, Kurnawa, Chikun Gudu, Tumbumma, Kwalaram, Kirta, Wulgo da Jubuladam

Borno - Bayan rashin manyan kwamandojin su da mayaka a luguden wutar da jiragen Super Tucano suka yi musu, shugabanni ISWAP sun yi sauye-sauyen mukamai.

PRNigeria ta ruwaito cewa, taron kwana biyun da suka yi tare da shugaban ISWAP, Sani Shuwaram, a cikin kwanakin karshen makon nan, ya samu halartar 'yan kwamitin Shura da kuma kwamandojin yankunan Marte da suka hada da Garal, Kayowa, Tumbum Murhu, Kurnawa, Chikun Gudu, Tumbumma, Kwalaram, Kirta, Wulgo da Jubuladam da sauran sansanonin gagararrun kwamandojin 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Borno: Bayan luguden Super Tucano, ƴan ISWAP sun sauya shugabanni
Borno: Bayan luguden Super Tucano, ƴan ISWAP sun sauya shugabanni. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin sabbin kwamandojin da aka nada sun hada da Abubakar Dan-Buduma wanda zai kula da yankin Bakassi Bunungil da Doron Buhari; Muhammad Ba'ana zai kula da yankin Kirta; Mohamet Aliamir zai kula da yankin Kwalaram; Bakura Gana zai kula da Jubularam; Malam Musa zai kula da Jubularam da kuma Mohamadu Mustapha zai kula da Marte.

Kamar yadda majiyoyi suka sanar, a taron an tattauna rashin kwamandoji da mayakan da aka yi sakamakon luguden da jirgin Super Tucano na sojin saman Najeriya yayi. Ya ragargagaji manyan ababen more rayuwarsu da suka hada da sansanin makamansu da kuma yankunan Marte da Abadam a Borno tare da wasu wurare na tafkin Chadi, Daily Nigerian ta ruwaito.

An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

Kara karanta wannan

Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a Gombe

A wani labari na daban, wani rahoton jaridar Daily Trust ya kawo cewa an harbe mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP da dama a arangamar da suke yi da dakarun sojojin Najeriya.

‘Yan ta’addan sun kai farmaki garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno a safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba.

Wata majiya ta sanar da jaridar cewa mayakan ISWAP sun kai farmakin ne da misalin karfe 9:00 na safe.

Sai dai abun bakin ciki, an rasa wani Birgediya Janar da wasu jami’ai a yayin da suke kare kasarsu amma kuma rundunar sojin kasa da na sama suna ta tayar da ‘yan ta’addan ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng