NDLEA ta kama tsoho, jami'in tsaron bogi da shigo da kwayoyi da Biskit Mai Ɗauke da Ƙwaya

NDLEA ta kama tsoho, jami'in tsaron bogi da shigo da kwayoyi da Biskit Mai Ɗauke da Ƙwaya

  • Hukumar NDLEA ta cika hannu da wasu masu yunkurin shigo da muggan kwayoyi Najeriya daga kasar waje
  • Daya daga cikin wadanda aka damke ya yi ikirarin cewa shi jami'in tsaro ne
  • Hakazalika akwai tsoho wannan ya goge wajen safarar ganyen Wiwi

Wani tsoho mai shekaru 76, Osagie Robert ya shiga hannun jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA a jihar Edo.

Tsohon wanda yafi shahara da sunan tsohon soja ya shiga hannu ne a ranar 7 Janairu, 2022 a Egor, ƙaramar hukumar Oredo da laifin safarar wiwi.

Wannan na kunshe a jawabin hedkwatar hukumar NDLEA ta saki ranar Asabar kuma Legit ta samu.

NDLEA ta kama tsoho, jami'in tsaron bogi da shigo da kwayoyi da Biskit Mai Ɗauke da Ƙwaya
NDLEA ta kama tsoho, jami'in tsaron bogi da shigo da kwayoyi da Biskit Mai Ɗauke da Ƙwaya
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: SERAP ta maka Lawan, Gbajabiamila a gaban kotu kan bata biliyan N4.1bn

Hakazalika hukumar ta ce ta kama Godwin Ilevbrave wanda ake yiwa inkiya da Edwin Agbon, jam'in tsaro na karya da laifin shigo da maƙulashe da biskit masu dauke da ƙwayoyi daga ƙasar Canada zuwa Nijeriya don sayarwa.

Godwin ya shiga hannu ne sanadiyyar tarko da jami'an hukumar suka yi masa ta hanyar aika saƙo ta kamfanin isar da saƙonni.

A lokacin da mai laifin ya sanya hannu a matsayin mai karɓan saƙon, jami'an hukumar ta NDLEA sun kama shi nan take a gidan sa dake birnin Benin a ranar talata 4 ga watan Janairu.

Saƙon wanda ya fito daga ƙasar Canada yana ƙunshe ne da sinadarin colorado na wiwi wadanda aka ɓoye su a cikin maƙulashe da biskit wanda nauyin su ya kai Kilogram 6.491, yayinda su kansu maƙulashe da biskit suke da nauyin 0.383kg.

An damke wani da hodar iblis

A wani labari mai kama da wannan, hukumar ta kama wani mai shekaru 48, Iloduba Augustine, fasinjan jirgi mallakar kamfanin ƙasar Habasha a filin jirgi na Akany Ibiam dake jihar Inugu.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Fasinjan wanda ya fito daga Sao Paulo, Ƙasar Brazil ya kasayar da ƙullin hodar Iblis guda 48 wadanda aka turowa wani ɗan Kenya akan hanyar sa ta zuwa Addis Ababa a bisa kuɗi Naira Miliyan ɗaya.

Mai laifin bayan ya shiga hannu ya bayyana cewa ya zo Nijeriya ne da sauran ƙulli goma a maƙoshin sa, wanda a cewar sa yayi niyyar sayarwa a Legas.

To amma bayan kama shi yayi kashin ƙulli-ƙulli na hodar Iblis ɗin da misalin ƙarfe 10:40am a ranar 1 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng