SERAP ta maka Lawan, Gbajabiamila a gaban kotu kan bata biliyan N4.1bn na majalisa

SERAP ta maka Lawan, Gbajabiamila a gaban kotu kan bata biliyan N4.1bn na majalisa

  • Kungiyar SERAP ta garazaya kotun tarayya dake zama a Abuja, ta nemi a tilasta wa shugabannin majalisa bincike kan batan biliyan N4.1bn
  • Wannan ya zo ne biyo bayan rahoton da ofishin Audita Janar ya fitar a 2016, inda ya nemi hukumomi su binciki yadda majalisa ta yi da kudin
  • A cewar SERAP, kundin tsarin mulki ya baiwa majalisa damar yaƙi da cin hanci da rashawa musamman wanda ya shafi yan majalisa

Abuja - Kunguyar SERAP mai fafutukar bin diddigin kuɗaɗen al'umma ta maka shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da kakakin majalisar dokoki, Femi Gbajabiamila, a gaban kotu.

Punch tace kungiyar ta ɗauki wannan matakin ne bisa gazawar shugabannin wajen bayanin yadda suka yi da biliyan N4.1bn, waɗan za aka ware wa majalisar tarayya.

Lamarin na zuwa ne biyo bayan fitar da rahoton shekara-shekara na 2016, wanda Audita Janar na kasa ya nuna, "Damuwarsa game da sama da faɗi da kudin ƙasa kuma ya nemi a bi ba'asin kuɗaɗen."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Shugabannin Majalisa
SERAP ta maka Lawan, Gbajabiamila a gaban kotu kan bata biliyan N4.1bn na majalisa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cikin shari'ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1609/2021, SERAP ta bukaci kotun tarayya dake Abuja, "Ta umarci Lawan da Gbajabiamila su sauke nauyin dake kansu wajen bincike kan zargin batan biliyan N4.1bn."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin majalisar tarayya na da alhakin yaki da rashawa?

Haka nan kuma kungiyar ta bayyana cewa doka ta dora wa majalisa alhakin hana cin hanci da rashawa da magance shi, da kuma gaskiya wajen tafiyar da dukiyar al'umma.

Vanguard ta rahoto wani sashin ƙarar yace:

"Alhakin majalisa ne ta taka rawa wajen yaki da almundahana matukar tana son aiwatar da kyakkyawan jagoranci, ta gudanar da bincike kan zargin cin hanci da sama da faɗi da dukiyar ƙasa musamman wanda ya shafi ɓangaren majalisa."

Bugu da ƙari, SERAP tace gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da dukiyar al'umma, sune jigon samar da cigaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Fusatattun Mambobin APC sun maka uwar jam'iyya da Gwamna Buni a gaban Kotu

"Majalisa ba ta da wani dalilin da zata fake da shi na ƙin gudanar da bincike kan rahoton zargi da ofishin Audita Janar ya fitar.

Lauyoyin ƙungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare, da Kehinde Oyewumi, su ne suka shigar da karar gaban kotu a madadin kungiya.

Har yanzun kotu ba ta sanya ranar da zata cigaba da sauraron wannan karar ba.

A wnai labarin kuma Shugaba Buhari ya sake caccakar majalisun tarayya kan sabon kundin zabe a tattaunawarsa da Channels TV

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake yin martani ga majalisar tarayya kan sabon kundin gyaran zabe 2021 da yaki sa wa hannu.

Shugaban yace ba zai yuwu a tilasta wa yan Najeeiya wata doka ba wajen fitar da gwani kuma ace ana mulkin demokaradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262