Hankula sun tashi a Jos yayin da aka sake tsintar gawar wata mace babu idanu da wasu sassa na jikinta

Hankula sun tashi a Jos yayin da aka sake tsintar gawar wata mace babu idanu da wasu sassa na jikinta

  • Mazauna yankunan Jos ta arewa da Jos ta kudu da ke jihar Filato sun shiga halin fargaba sakamakon kisan wasu mata biyu
  • An tsinci gawar wacce aka kashe ta baya-baya mai suna Plangnan Solomon a yankin Rayfield da ke karamar hukumar Jos ta Kudu bayan an cire mata idanu da wasu sassa na jikinta
  • Ana zaton dai masu asiri ne suka yi wannan aika-aika, inda aka bukaci mazauna yankunan musamman mata da su yi taka-tsan-tsan

Filato - An tsinci gawar wata mazauniyar yankin Congo Russia, a karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Filato.

An yasar da gawar matashiyar mai suna Plangnan Solomon a kusa da shahararren gidan radiyon nan na Plateau Radio Television Corporation (PRTV), a yankin Rayfield da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Hankula sun tashi a Jos yayin da aka sake tsintar gawar wata mace da aka yi asiri da ita
Hankula sun tashi a Jos yayin da aka sake tsintar gawar wata mace da aka yi asiri da ita Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An samu gawarta ne a yankin inda aka kwakule mata idanu sannan aka yanka wasu sassa na jikinta.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Victor Kwara, wani shugaba a Congo Russia, ya tabbatar da lamarin a ranar Juma'a, 8 ga watan Janairu, inda ya kara da cewar an binne ta.

Lamarin na zuwa ne bayan Premium Times ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan jihar Filato ta hannun kakakinta, ASP Ubah Geberiel, ta tabbatar da kisan wata mata a masaukin bakin Domus Pacis, hanyar Zaria Road na karamar hukumar Jos ta arewa.

Kisan matan biyu ya jefa mazauna yankunan Jos ta arewa da Jos ta kudu cikin rudani inda wasu da dama ke zargin cewa masu asiri sun taru a jihar.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Shugaban garin ya yi kira ga mazauna jihar musamman mata da su kula sannan su yi taka-tsan-tsan da irin mutanen da suke mu'amala da su.

Babbar Magana: Tashin hankali yayin da gawa ta yi batan dabo a dakin ajiye gawa ranar biso

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan uwan wata mata da ta kwanta dama sun shiga halin tashin hankali yayin da gawar matar ta yi batan dabo a dakin ajiye gawa a jihar Ebonyi.

Ba a samu damar yin bikin binne gawar ba sakamakon batan gawar, jaridar The Nation ta rahoto.

A cewar rahoton, an ajiye gawar marigayiya Madam Grace Orjiokoro a dakin ajiye gawa na babban asibitin Owutu Edda a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke jihar bayan ta mutu a asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng