Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari
- Kungiyar matasan Tiv ta yi kira ga Gwamna Samuel Ortom da ya mayar da hankali wurin aikin mulkin jiharsa a maimakon sukar Buhari
- Kungiyar ta sanar da cewa, jihar Benue ta samu ci baya na fiye da shekaru 20 karkashin mulkin Ortom wanda ya zame musu kadangaren bakin tulu
- Har ila yau, kungiyar ta ce dukkan ma'aikatun jihar suna dandana wahala da zaba inda 'yan fansho suka shiga mawuyacin hali
Benue - Kungiyar matasan Tiv ta fadin duniya ta yi kira ga gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da ya mayar da hankali wurin dawo da sunansa da bunkasa walwalar ma'aikata a jihar fiye da "amfani da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kanun labarai".
Shugaban kungiyar matasan Tiv, Honarabul Mike Msuaan, ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga amsar da Ortom ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tattaunawa da ChannelsTV.
Daily Trust ta ruwaito cewa, sanannen abu ne cewa gwamna Ortom ya kawo wa jihar Benue ci bayan shekara 20 sannan ya zama kadangaren bakin tulu ga cigaban jihar, kungiyar tace.
Kungiyar ta lura da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gwamnan yana magana ne kamar shi dan kasa ne kawai bayan ya manta shi ke da alhakin bada tsaro ga kasar kuma aikinsa ne ya tsaro gami da kawo cigaba da kula da lafiyar mutanen jihar Benue.
"Kamar gwamnan ya manta cewa shine kadai gwamna a tarihin Najeriya da yabar masu amsar fansho suna bacci a kofar gidan gwamnatin na tsawon makwanni 2 suna zanga-zanga game da jinkirin biyansu kudin fansho da garatuti da aka yi. Yunwa ta tilasta masu amsar fanshon suka bar gidajensu,suka zabi su mutu a kofar gidan gwamnatin.
"A karkashin gwamna Ortom, talauci ne yayi zaman dirshan a hedkwatoci a jihar. Yayin da ya gaza biyan ma'akata da masu amsar fansho a jiha mai cike da ma'aikatan gwamnati, talauci yayi wa mutane rub da ciki, ta kai ga basu samun abincin da zasu sa a bakin salatinsu da tufatantar da iyalansu.
Ma'aikata a jihar basu morar mafi karancin albashi da gwamnati ta maida duk da irin yamadidin da akai tayi da gwamnati ta yi umarnin "gaggauta biyan mafi karancin albashi da gwamnati ta kawo ga ma'aikata."
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Ortom ya fara sukar Buhari ne bayan gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga da matsayin yan ta'adda, yayin da yace sai dai ya ambaci Miyyetti Allah, MACBAN da kungiyoyin fulani na kasa a matsayin 'yan ta'adda.
Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kiran ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.
A wata takarda wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur ya saki, ya yanko inda gwamnan ya ce kungiyar tana kawo tashin hankali a Binuwai.
Asali: Legit.ng