Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin mambobin kwamitin jagorancin NNPC
- Bayan yan kwanaki da sanar da nadinsu, Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwan NNPC
- Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya zama kamfani mai zaman kansa tun bayan kafa sabuwar dokar PIA
- Yan Najeriya na zaman jiran tsammanin karin farashin man fetur da Gwamnati tayi alkawarin za tayi a sabuwar shekara
FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya rantsar da sabbin mambobin kwamitin jagorancin kamfanin man feturin Najeriya NNPC.
Shugaba Buhari ya rantsar da su ne a farfajiyar majalisar zartaswa dake fadar Aso Villa, Abuja.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.
A cewarsa, Shugaba Buhari ya yi kira da sabbin jagororin su mayar da hankali kan samar da riba mai tsoka don amfanin Najeriya.
Yace:
"An bukaci kamfanin NNPC ya mayar da hankali kan samar da kudi da kuma kokari bayan cika sharrudan dokokin kafa ta."
"Ana sa ran NNPC zai yi aiki kamar ire-irensa na fadin duniya, tare da zama kamfanin da zai samar da cigaba da sassan tattalin arzikinmu."
"Wannan rantsarwa babban mataki ne wajen samar da masana'antar man fetur da zai janyo hankalin masu zuba jari don taimakon cigaban tattalin arziki da samar da aikin yi ga miliyoyin mutanenmu."
Karamin Ministan mai, Timire Sylva, a nasa jawabin, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama a bangaren man fetur.
Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara
Kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur ma da sunan cire tallafin mai.
NLC ta yi kira ga ma'aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi.
Shugaban NLC, Ayuba Wabbab, ya bayyana hakan a jawabin sabon shekara da ya saki ranar Asabar.
Ayuba Wabba ya lissafa jihar Zamfara, Taraba, Benue, Kogi, Cross Rivers, Abia da Imo matsayin jihohin da har yanzu basu biyan ma'aikata mafi karancin albashin N30,000.
Asali: Legit.ng