Khalifan Tijjaniyya na duniya da sauran manya sun wuce taron Zikirin da SLS ya shirya, sunki zuwa na Ganduje
- Shugaban darikar Tijjaniyya, Sheikh Niasse da sauran manya a Tijjaniya sun ki zuwa taron zikirin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya na ranar Juma’a
- Majiyoyi sun bayyana yadda su ka wuce taron da tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya shirya a Lokoja duk da taron ya zo rana daya da na Ganduje
- An samu labarai akan yadda gwamna Ganduje ya tura jirgi na musamman ciki har da Sheikh Dahiru Bauchi don su je har Kaulaha su gamsar da Khalifan ya halarci nasa taron
Khalifan Tijjaniyya na duniya, Sheikh Mahy Niasse da sauran manyan shugabannin Tijjaniyya sun ki zuwa taron zikiri wanda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya a fadar sarkin Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.
Zikiri taro ne wanda malamai sufaye su ke yi don addu’o’i, kuma ana sa ran za ayi shi ne a ranar Juma’a.
Majiyoyi sun ce taron na Kano ya zo rana daya da wani zikiri na Lokoja wanda sabon shugaban darikar Tijjaniyyar na Najeriya kuma tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya shirya.
Majiyoyi daga ciki sun sanar da Daily Nigerian cewa gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano ne su ka shirya duk don su kaskantar da mulkin Sunusi a kungiyar kuma don su samar da rabuwar kawuna cikin masu matsayi a Tijjaniyya.
Har malamai Ganduje ya tura Senegal don gamsar da Khalifan Tijjaniyya akan halartar zikirin nasu
Kamar yadda wata majiya ta shaida:
“Gwamnatin jihar Kano ta tura jirgi na musamman wanda ya dauki Sheikh Dahiru Bauchi da dansa Ibrahim; Isah Bayero da sauran manya a gwamnati zuwa Kaulaha da ke kasar Senegal don su gamsar da babban Khalifa na Tijjaniyyar duniya, Sheikh Mahy Niass don ya halarci taron zikirin na Kano.
“Amma bayan gano cewa an gayyace shi zuwa Kano ne saboda a bata wa Sunusi rai tare da kawo rabuwar kawuna ga kungiyar a Najeriya, Sheikh Mahy ya ki amincewa da gayyatar tasu kuma ya ki tura wakilai.
“Sun garzaya wurin babban limamin Kaulaha, Sheikh Tijjani Cisse, shi ma ya ki amsar gayyatar tasu.”
Sheikh Mahy ya tura wakilai 22 zuwa zikirin Sunusi
Daily Nigerian ta gano cewa Khalifan Tijjaniyya ya amshi gayyatar taron zikirin da Sunusi ya shirya wanda za ayi a Lokaja kuma ya tura taron maza 22 wanda mataimakin Khalifan na duniya, Sheikh Muhammadu Lamin Niyass ya jagoranta a matsayin wakilai.
Majiyoyi sun ce ana sa ran duk wasu shugabannin Tijjaniyya na Najeriya ban da Sheikh Dahiru Bauchi, za su halarci taron zikirin na Lokoja.
Yanzu haka duk su na cikin garin Lokoja ciki har da Sheikh Maihula, Sheikh Kafinga, Sheikh Salga, Sheikh Tuhami, Sheikh Abdullahi Uwais tare da Sheikh Ibrahim Maqary, Sheikh Manzo Arzai da Sheikh Gwammaja duk sun ki zuwa zikirin Kano saboda na Lokoja.
Ganin abinda ke shirin faruwa wanda shugabanni su ka ki zuwa nasu taron, gwamnan ya je Algeria inda ya dauko magadan wadanda su ka kirkiri darikar Tijjaniyya, Sheikh Ahmad Tijani, wanda shi ma ya ke ikirarin shugaba ne a darikar.
A ranar Alhamis, Ganduje da sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tarbi wani shugaba na darikar, Sheikh Ali bn Arabi daga Algeria.
Yayin da Daily Nigerian ta bukaci jin ta bakin kakakin Ganduje, Abba Anwar, ya ce a tuntubi kwamishinan harkokin addini, Tahar Adam.
Sai dai Adam ya ki cewa komai dangane da lamarin inda yace ba zai yi magana da dan jarida ta waya ba.
Dan Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ziyarar da mahaifinsa ya kai Kaulaha ba ta da alaka da gayyatar kowa zuwa taron Kano
Aminu Dahiru Bauchi, wanda ya yi magana a maimakon mahaifinsa ya ce ziyarar da mahaifinsa ya kai Kaulaha ba ta da alaka da gayyatar Sheikh Mahy zikirin Kano saboda duk sanda ya so yana zuwa.
Daily Nigerian ta gano cewa an yi iyakar kokarin ganin an dakatar da taron Lokoja amma abin ya ci tura.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya sanar da shugabbannin Tijjaniyyar da su ka kai masa ziyara gidan gwamnati cewa an so a sa shi ya dakatar da taron da Sunusi ya shirya amma ya ki.
Sai dai gwamnan bai bayyana wanda ya yi kokarin dakatar da shi ba amma zai yuwu wani abokin aikinsa ne wanda ya ke da jikakkiya da sabon Khalifan
Asali: Legit.ng