Izala ta dakatar da Jalo Jalingo daga tabo mas'alar makomar iyayen Annabi, ta bada sharuda 5
- Kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah tayi zama na musamman da Ibrahim Jalo Jalingo
- An yi wannan tattaunawa ne a dalilin karatun da Dr. Jalo Jalingo yake yi a kan makomar iyayen Annabi
- JIBWIS tace a daina bijiro da irin wannan mas’alar a gaban gama-garin al’umma domin gudun jawo rudani
Abuja - Shugabanni da manyan malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) sun yi zama da Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.
Rahoton da muka samu daga shafin JIBWIS na Facebook ya bayyana cewa an zauna da malamin ne a game da karatun da yake yi wanda ya jawo maganganu.
Shehin malami Ibrahim Jalo Jalingo ya na tabo batun makomar iyayen Annabi Muhammad SAW. Akwai sabani sosai a kan wannan mas’ala a addinin musulunci.
Ana sa ran wannan zaman zai taimaka wajen samar da hadin-kai da kauracewa rudani a al’umma.
A karshen wannan zama da aka yi a sakatariyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah da ke birnin tarayya Abuja, an yi nasarar cin ma wasu matsayoyi biyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sharudan da JIBWIS ta kakaba
Daga ciki shi ne an bukaci malamin ya dakatar da duk wani bayani ko rubutu a game da wannan mas’ala a cikin gama-garin mutane saboda gudun a kawo rudani.
Kungiyar Izala ta kuma yi umarni ga malamanta cewa a rika tattauna duk wata mas’ala ta ilmi a majalisar malamai kafin a bijiro da ita a cikin sauran al’umma.
Bayan haka an umarci a janye duk wasu karatuttuka da aka gabatar a game da wannan mas’ala a kafofin sadarwa na zamani domin gujewa sabanin rashin fahimta.
Wani mataki da aka cin ma a wannan zama da aka yi a ranar Laraba, 5 ga watan Junairu, 2022 shi ne kira ga al’umma su dukufa wajen addu’ar zaunar da kasa lafiya.
Sanarwar tace a karshe kungiyar ta roki Allah (SWT) ya kara mana son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam (SAW), Ya hada kan malamai bisa Qur’ani da sunnah.
Mutuwar Bashir Tofa
A makon nan ne aka ji cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi ya yi wa jama’ar Kano da daukacin mutanen Arewa ta’aziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa.
Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II yace mutuwar Dattijon rashi ne ga Najeriya gaba daya, yace ya rasa mutumin da yake kaunarsa da shi da zuri'arsa.
Asali: Legit.ng