An tsinci gawar wata mata a cikin wani otel a Jihar Filato
- An tsinci gawar wata mata a cikin otal din Domus Pacis da ke kan titin Zaria a karkashin karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Filato
- Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel ya shaida, an tsinci gawar ne cikin jini a daki mai lamba 302 da ke Otal din
- Har yanzu dai ‘yan sanda su na ci gaba da bincike don gano asalin silar mutuwar tata da kuma wanda ya ke da alhakin aiwatar mata da mummunan aikin
Jihar Filato - An tsinci gawar wata mata a cikin Otal din Domus Pacis da ke kan titin Zaria karkashin karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Plateau, Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel ne ya shaida cewa an tsinci gawar jina-jina a cikin daki mai lamba ta 302 cikin otal din.
Sun dauki hotunan gawar
Kamar yadda dan sandan ya shaida:
“A ranar 1 ga watan Janairun 2022 da misalin karfe 3:30 na rana, rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta samu mummunan labari akan yadda aka tsinci gawar wata mata a cikin jini a wani masaukin baki na Domus Pacis, cikin daki mai lamba ta 302 a kan titin Zaria Road cikin garin Jos.
“Bayan samun rahoton ne kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bartholomew Nnamdi Onyeka, psc(+), ya tura rundunar ‘yan sanda wurin da lamarin ya faru inda su ka dauki hotunan gawar sannan aka zarce da ita asibiti don binciken silar mutuwarta.”
Har yanzu ana ci gaba da bincike
Daily Trust ta ruwaito cewa ASP Gabriel ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike don gano silar mutuwar ta da wadanda suke da hannu a yin aika-aikar.
Ya kara da shaida cewa kwamishinan ‘yan sanda ya kira taron gaggawa inda ya koya wa ‘yan sandan dabarun da zasu bi don tabbatar da kwatankwacin hakan bai sake aukuwa ba a wani otal.
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng