Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

  • Shugaban kasa ya yi kira ga matasan Najeriya da suka kammala karatu su tashi tsaye su nemawa kansu abinci
  • Buhari ya ce ana zuwa makaranta ne don ilimi da wayewa ba don samun aikin gwamnati kadai ba
  • Ya kara da cewa tunanin cewa idan ka kammala karatu zaka sayi mota kayi gini gurgun tunani ne

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya suyi amfani da ilmin da suka samu a makaranta da wayewa wajen inganta kawunansu sabanin dogaro kan aikin gwamnati.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hira ta musamman da gidan talabijin ChannlesTV ranar Laraba.

"Na so idan suka je makaranta; suka yi kokari; suka samu digiri, kada suyi tunanin dole ne sai gwamnati ta basu aiki," ya bayyana.

"Ka nemi ilimi ne saboda mai ilimi ya fi mara shi, ko wajen fahimtar matsalolin kai. Saboda haka ba a neman ilimi don gwamnati ta bada aiki ko kuma abinda turawan mulkin mallaka suka dasa mana a kai na cewa sai ka yi mota, ka yi gini, kana zuwa aiki karfe 8 ka dawo karfe 2."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya
Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan haka, Buhari ya yi magana kan wasu lamura wanda ya hada da rashin rattafa hannu kan dokar zabe.

Buhari ya ki rattafa hannu kan dokar saboda tsarin yar tinke da aka sanya cikin dokar.

A hirar, ya ce zai rattafa hannu muddin majalisar dokokin tarayya tayi gyaran da ya kamata.

"Abinda na fadi shine a baiwa mutane zabi. Bai kamata mu ce wajibi ne ayi yar tinke ba; ya kamata akwai ittifaki da na deleget."

Yayinda aka tambayesa ko zai rattafa hannu idan yan majalsan suka yi canjin, ya tabbatar da cewa, "A zan yi, zan rattafa hannu."

"Ya kamata akwai zabi, ba zai yiwu ku yiwa mutane kama karya ba kuma kuce kuna demokradiyya. Ku basu wasu zabin saboda su zaba."

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yiwa yan Najeriya iyakan kokarinsa kuma yana sa ran idan ya sauka daga mulki zasu fadi hakan da kansu.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa a gidan talabijin na NTA da aka haska ranar Alhamis.

Buhari yace:

"Abinda nike sa ran yan Najeriya suce shine mutumin nan ya yi iyakan kokarinsa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng