Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana maraba da duk wanda ya shirya taimaka wa Najeriya ta samu ababen more rayuwa
- Buhari ya ce karbar bashin da ake yi daga China shi ne yasa ake samun ababen more rayuwa, kuma koyaushe bukatar hakan ta taso, za a karbo
- Shugaban kasar ya ce da ba don basussukan da aka karba ba, da yanzu babu tituna a kasar nan, Legas zuwa Ibadan a kasa 'yan Najeriya za su dinga zuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kare gwamnatinsa kan hukuncinta na karbo basussuka daga China, ya ce duk wanda zai taimaka wurin samarwa da Najeriya ababen more rayuwa ana maraba da shi.
Kamar yadda bayanin da Ofishin kula da basussuka ya sanar, Najeriya ta aro $2.02 biliyan a matsayin bashi daga China daga 2015 kuma bashin kasar nan ya kai $3.40 biliyan daga China a ranar 31 ga watan Maris na shekarar da ta gabata.
A yayin jawabi a tattaunawar da suka yi da Channels TV, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa duk lokacin da bukatar karbo bashi daga kasar waje ta taso, gwamnatinsa za ta yi hakan.
Shugaban kasan ya kara da kokarin goge tsoro daga zukatan wasu 'yan Najeriya na cewa kasar nan za ta iya fadawa cikin matsanancin bashi.
"Muna karbar bashi inda ya dace. In fada muku wani abu yanzu, abinda ke tsakanin Legas da Ibadan kadai ba wai sauran kasar nan ba abun mamaki ne," yace.
“Amma mun samu 'yan China da za su taimaka mana da titunan jirgin kasa da na motoci, ta yaya za mu ki hakan? Da a ce mun ki amincewa, da yanzu kila a kafa za ku dinga takawa daga Legas zuwa Ibadan.
“Don haka muna maraba da 'yan China, duk wanda ya shirya kuma zai taimake mu da ababen more rayuwa kamar tituna, layin dogo da wutar lantarki, duk muna maraba".
Buhari: Na san baƙar uƙuba da tsabar wahalar da ƴan Najeriya ke ciki
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya ce ya na sane da bakar ukuba da kuma tsabar wahalar da 'yan Najeriya suke shiga kafin su ciyar da kansu da iyalansu a karkashin mulkinsa.
Shugaban kasan wanda ya sanar da hakan yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels, ya kara wa mutane karfin guiwa da su duba noma da kiwo a matsayin mafita.
"Tabbas na san wahalar da mutane suke ciki," yace. "Amma kamar yadda nace, ku kalla yawan 'yan Najeriya, kashi 2.5 na kasa ne ake nomawa.
Asali: Legit.ng