Kotun Shari'a ta umarci mata ta tattara komatsanta ta bar gidan tsohon mijinta cikin sa’o’i 72 a Kaduna

Kotun Shari'a ta umarci mata ta tattara komatsanta ta bar gidan tsohon mijinta cikin sa’o’i 72 a Kaduna

  • Wata kotun Shari’ar musulunci mai zama a Magajin Gari, Kaduna ta umarci wata mata, Rahma Usman, da ta tattara komatsanta ta bar gidan tsohon mijinta, Abdulbasit Sulaiman cikin sa’o’i 72
  • Alkalin, Malam Murtala Nasir ya bayar da wannan umarnin a zaman kotun da su ka yi bayan tabbatar da rabuwar auren tsakanin ma’auratan
  • Sannan alkali ya bukaci Sulaiman ya dinga biyan tsohuwar matar tasa, N10,000 har sai ta kammala zaman iddanta

Kaduna - A ranar Laraba wata kotun shari’ar musulunci mai zama a Magajin Gari ta umarci Rahma Usman da ta kwashe kayanta ta bar gidan tsohon mijinta, Abdulbasit Sulaiman cikin sa’o’i 72, The Nation ta ruwaito.

Alkalin, Malam Murtala Nasir, ya bayar da wannan umarnin bayan kammala shari’ar da ke tsakaninsu wacce ya tabbatar da rabuwar aurensu.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Alkalin ya umarci Sulaiman da ya dinga biyan tsohuwar matarsa N10,000 ko wanne wata a matsayin kudin ciyarwa har ta kammala zaman iddarta.

Kotu ta bawa wata mata awa 72 ta tattara komatsenta ta fice daga gidan tsohon mijinta
Kotu ta umurci mata ta fice daga gidan tsohon mijinta cikin awanni 72. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Mijin ne ya fara kai karar matar kotu

Dama Suleiman ne ya maka karar tsohuwar matar tasa a watan Nuwamban 2021 inda ya bukaci kotu ta umarce ta da ta bar gidansa kuma yace ta kammala zaman iddanta.

The Nation ta ruwaito yadda ya bayyana cewa ya sake ta tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.

Zaman Iddah ta ke yi, in ji lauyanta

Lauyan wacce ake kara ya ce bata kammala zaman iddanta ba kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, hakan ya sa ta ci gaba da zama a cikin gidan tsohon mijin nata.

A cewar lauyan:

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

“Wacce nake karewa ta ga hailarta na tsawon watanni biyu kenan, don haka bata kammala iddarta ba.”

NAN ta ruwaito cewa idan mata ta rabu da mijinta, za ta zauna a gidansa ne har sai ta ga hailarta ta ko wacce wata na watanni uku, hakan ake kira Iddah, sannan ta sake wani auren.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Kara karanta wannan

Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane, APC ta yi wa Shehu Sani martani

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164