Babbar Magana: Wata mummunar wuta ta yi barna a majalisar dokokin jihar Katsina

Babbar Magana: Wata mummunar wuta ta yi barna a majalisar dokokin jihar Katsina

  • Wata Gobara da ta tashi a majalisar dokokin jigar Katsina ranar Lahadi da daddare ta yi wa zauren barna sosai
  • Kakakin majalisar dokokin, Honorabul Maigari, yace jami'an hukumar kashe gobara sun ɗauki matakin gaggawa domin kare munin lamarin
  • Yace majalisa ta kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan musabbabin da ya tada gobarar

Katsina - Gobara ta kone wani sashin zauren majalisar dokokin jihar Katsina watanni takwas bayan zauren ya yi fama da matsala makamanciyar wannan.

Kakakin majalisar dokokin, Honorabul Tasi'u Maigari, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, yace wutar ta yi barnan ne ranar Lahadi da daddare.

A rahoton jaridar Vanguard, kakakin majalisar yace wutar ta taba ofishin magatakardan majalisa, mataimakinsa da kuma dakin yan majalisu.

Lamarin Gobara
Babbar Magana: Wata mummunar wuta ta yi barna a majalisar dokokin jihar Katsina Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

Honirabul Maigari yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bangaren Sheikh Gumi ya maida zazzafan martani kan kashe shugabannin yan bindiga a Zamfara

"Wutar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Lahadi, amma jami'an hukumar kashe gobara sun yi gaggawar kawo ɗauki suka kashe ta domin kare yaduwarta."
"Mun kafa kwamiti bisa jagorancin shugaban gida, Abubakar Suleiman Abukur, domin binciko musabbabin tashin gobarar da sauransu."

Shin wutar ta yi mummunan barna ne?

Duk wani kokari na shiga zauren domin gano ainihin barnan da wutar ta yi bai yi nasara ba, domin ma'aikata sun hana shiga ofisoshin da lamarin ya shafa.

A cewarsu, an umarce su kada su kuskura su bari a ɗauki hoto ko bidiyon ofisoshin da gobarar ta shafa.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa wutar ta tashi ne daga wutar lantarki, kuma ta fara ne daga ofishi daya sannan ta cinye kusan ofis biyar, ta lalata takardu da wasu kayayyaki.

A wani labarin na daban kuma Bayan cikar watanni uku, Gwamna El-Rufa'i ya kara wa'adin hana Acaba a jihar Kaduna

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Gwamnatin Kaduna ta kara wa'adin hana Okada, yawo da makami da sauran matakan da ta ɗauka har sai baba ta gani.

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, yace matakan na nan daram har sai gwamnati ta fitar da sanarwa nan gaba kan matakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262