Mun samu izinin fara amfani da jiragen 'Super Tucano' wajen ragargazan yan bindiga, Ministan Shari'a
1 - tsawon mintuna
- Abubakar Malami ya bayyana cewa Najeriya ta nemi izini wajen Amurka don amfani da jiragen Super Tucano
- Najeriya ta sayi jiragen Suer Tucano guda shida don yakar yan ta'addan Boko Haram dake Arewa maso gabashin Najeriya
- Yanzu Gwamnati na son fara amfani da jiragen wajen ragargazan yan bindiga a Arewa maso yamma
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta samu izinin fara amfani da sabbin jiragen 'Super Tucano' wajen ragargazan yan bindiga masu garkuwa da mutane a fadin tarayya.
A shekarar 2021, Gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jirage daga kasar Amurka.
Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN, ya bayyana hakan a shirin Good Morning Nigeria na tashar NTA ranar Talata, 4 ga Junairu, 2022.
Yace Gwamnatin tarayya ta samu izini daga wajen Amurka kuma ta yi alkawarin amfani da jiragen yadda ya kamata.
Yace yanzu haka ana kokarin katabta jiragen cikin kundin dokokin Najeriya.
A cewarsa:
"Muna fuskantar matsalar yan bindiga a Arewa maso yamma kuma shi yasa muka sayi makamai wajen yaki da su."
"Mun samu izinin amfani da Super Tucano. Yanzu muna shirin katabtashi cikin doka."
Asali: Legit.ng