Majlisar koli ta Shari'ah ta nada Abdurrashid Hadiyatullahi matsayin shugaban ta
- Majalisar kolin kotun shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) ta nada AbdurRashid Hadiyatullah a matsayin shugabanta
- Majalisar ta sanar da nadin nasa ne a ranar Litinin bayan kammala wani taro wanda suka yi a garin Kaduna
- Nadin Hadiyatullah ya biyo bayan mutuwar Ibrahim Ahmed Datti, tsohon shugaban SCSN da ya rasu a jihar Kano
Majalisar koli ta shari’ar musulunci ta Najeriy, (SCSN) ta sanar da nada AbdurRashid Hadiyatullah a matsayin sabon shugaban ta.
TheCable ta ruwaito cewa, majalisar ta sanar da nadin ne ranar Litinin bayan kammala wani taro wanda su ka yi a Kaduna.
Nadin Hadiyatullah ya biyo bayan kwanaki kadan da mutuwar Ibrahim Ahmad Datti, tsohon shugaban SCSN, TheCable ta ruwaito.
Kamar yadda majalisar ta saki a wata takarda, Hadiyatullah ya rike kujerar mataimakin shugaban majalisar inda ya yi aiki tare da marigayi shugaban.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Majalisar ta shiga damuwa sakamakon rashin daya daga cikin jagororinta, Ibrahim Datti Ahmed, wanda har ya rasu yana kan kujerar shugaban majalisar. Muna masa fatan samun rahama da kuma Aljannar Firdausi,” kamar yadda takardar tazo.
“Yayin da muke takaicin wannan rashin, tare da mika dukkanin godiya ga Allah tare da bin dokar kundin tsarin mulki, Sheikh AbdurRashid Hadiyatullah, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar, ya zama shugaban majalisar koli ta shari’ar musuluncin Najeriya.
“Mu na fatan Allah SWT ya ba shi fasaha da jagoranci wurin isar da manufar majalisar musamman samar da hadin kai da ci gaba al’umma.”
Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa
A wani labari na daban, Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ahmad, rasuwa ranar Alhamis a jihar Kano.
Diraktan tashar Sunna TV, Dr Abu Aisha Ibrahim Disina a jawabin ta'aziyyarsa ya bayyana cewa za'a yi Sallar jana'iza a Masallacin Al-Furqan dake Kano misalin karfe 10 na safe. Ya siffanta marigayin a matsayin dan gwagwarmayan kare Musulmai a Najeriya.
A cewarsa:
"Gwagwarmayar kare muradun Musulmai ba za ta manta da kai ba a Nigeria!! Janaza: 10:00am a Masallacin Alfurqan Kano. Allah ya karbi aiyukanka, Ya kai haske kabarinka, Ya sanya Aljannah ce Makomarka. Allah ka kiyayemu, mu 'yan baya, Ya sa mu cika da Imani."
Asali: Legit.ng