Bidiyon katafaren gida da maza 4 suka gina da taɓo a ƙauye, har da wurin wanka mai ƙayatarwa
- Wasu maza hudu 'yan kasar Cambodia sun matukar bai wa jama'a mamaki da irin aikinsu ta yadda suka yi amfani da kasa wurin hada gida
- Daya daga cikin manyan ayyukansu masu bayar da sha'awa shi ne yadda suka gina katafaren gida a kauye wanda komai a cikin gidan aka yi shi da kasa
- Molly, mutumin da ya tattara maginan, ya ce sun kwashe shekara daya tare da kashe wasu kudade kafin su samu su hada gidan da ke da wurin wanka
Wasu hazikan maza 'yan asalin Cambodia sun kawo wani sabon salo na hada kayayyaki da kasa inda suka gina gida kacokan da kayan cikinsa da kasa.
Nas Daily ta wallafa bidiyon a Facebook na yadda katafaren gidan kauyen ya hadu kuma ya kunshi wurin wanka, kujerun kasa da sauran kayayyakin amfanin gida.
Sun yi amfani da kayayyakin gargajiya wurin yin ginin
A yayin bayani ga Nas Daily, mutumin mai suna Molly ya ce ya lura da yadda 'yan Cambodia ke da fasahar kirkire-kirkire, hakan yasa ya yi amfani da wannan hazakar domin nuna ayyukansu ga duniya a YouTube.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Molly magini ne wanda ke zama a kasar Cambodia, ya kara da cewa ya nemo magina masu amfani da kasa wadanda ke zama a daji kuma ya ba su tsarin ginin wanda suka fitar ya yi kyau.
Mazan hudu sun kware wurin hako kasa tare da amfani da kayayyakin gargajiya wurin hada abubuwa masu siffa daban-daban.
Kirkirarsu ta janyo hankulan masu yawon bude ido
Gini tare da kirkirar katafaren gidan kasan ya kwashe wurin shekara daya kuma ya lamushe dubban daloli.
Gidajen da suka gina babu mutum da ke zama, karnuka da 'ya'yansu ne ke zama kuma masu yawon shakatawa da bude ido sun gane wuraren.
Molly ya ce, abun takaici ne yadda gidajen ke iya tsayuwar shekara daya kacal kafin ruwa ya rushe su ko kuma wani abu na daban.
Jama'a sun yi martani
Paul Njenga ya ce:
"Ban taba yadda cewa mutane suna da hazaka kamar haka ba. Wasu sai sun je jami'a domin koyo amma wasu kuwa Allah ne ke basu. A rayuwa, wasu sai sun je makaranta za su samu madogara, amma wasu kuwa da hazakarsu suke samun madafa."
Danica Joy Castañeda-Monreal ya rubuta:
"Ina fatan mazan nan ana biyansu kudi isasshe kuma suna samun wurin zama domin yin rayuwarsu cike da kwanciyar hankali. Ko kuma suna samu magani saboda na lura wani idonsa ba daidai ya ke ba. Su ne suka yi dukkan aiki kuma sun cancanci jinjina."
Bidiyon dan achaba dauke da fasinjoji 7 reras ya janyo cece-kuce
A wani labari na daban, wani dalili na iya janyo wa mutum ya kirkiro abinda ba a taba gani ba, amma wannan kirkirar babur din na musamman ya shayar da mutane da dama tsananin mamaki.
A wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga yadda wani mutum ya ke tuka wani babur mai doguwar kujera.
Shafin goldmynetv ya wallafa bidiyon a Instagram, kuma an ga wani babur da zai iya daukar mutane 8 inda daya zai kasance mai tuki yayin da sauran wurin zai isa fasinjoji 7 duk a lokaci guda.
Asali: Legit.ng