Masari ya magantu kan labarin garkame dan jarida da ya bayar da umarni

Masari ya magantu kan labarin garkame dan jarida da ya bayar da umarni

  • Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya tabbatar da cewa ba shi da masaniya akan garkame wani dan jarida
  • Abdu Labaran, darekta janar na labarai ga gwamnan ya sanar da hakan ta wata takarda wacce ya saki a Katsina ranar Lahadi da dare
  • Ya yi magana ne akan takardar da kungiyar ‘yan jarida ta kasa ta saki tana zargin gwamnan da umartar kama wani dan Jarida

Katsina - Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce ba ya da masaniya akan kamun wani dan jarida, Daily Nigerian ta ruwaito.

Masari ya ce bai umarci wani ma’aikacinsa ya kama dan jaridar ba kamar yadda darekta janar na labarai ga gwamnan ya sanar ta wata takarda a ranar Lahadi da dare a Katsina.

Masari ya magantu kan labarin garkame dan jarida da ya bayar da umarni
Masari ya magantu kan labarin garkame dan jarida da ya bayar da umarni. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Labaran ya saki takardar ne don bayar da martani ga zargin da kungiyar ‘yan jarida ta kasa, NUJ da ta yi wa Masari tana zarginsa da kama wani Nelson Omonu ma’aikacin jaridar Summit Post.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

“An janyo hankalin gwamnatin jihar Katsina akan wata takarda da kungiyar ‘yan jarida, NUJ, ta yankin FCT, wacce ta zargi gwamnan da bayar da umarnin kama wani Nelson Omonu, ma’aikacin jaridar Summit Post.
“Yau aka saki takardar wacce kwamared Emmanuel Ogbeche da Ochiaka Ugwu, shugaba da kuma sakatarn kungiyar su ka sa hannu.
“Sun zargi cewa jami’an tsaron da ake zargin su na aiki da umarnin Masari sun kwashe dan jaridar.
“Abin ban takaici shine yadda FCT NUJ suka yi munanan kalamai akan rashin tsaron da jihar Katsina ke fuskanta kamar ita ce kadai jihar da take fama da ta’addanci.
“Don fadada bayani, gwamnan jihar Katsina ko kuma wani ma’aikaci da gwamnatin jihar bai bayar da umarnin kama wani dan jarida ba a Abuja ko wani wurin daban,” kamar yadda wani bangaren takardar yazo.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Gwamnan ya kara da cewa akwai ‘yan jarida da ke aiki a Katsina da kuma wasu da ke aiki a wasu yankuna na kasar nan, duk ba a kama su ba sai shi, kamar shi ne kadai ma’aikacin jarida a Najeriya.

“Ga dukkan alamu, munanan maganganun da shugabannin ‘yan jaridan FCT sun nuna rashin sanin aikin ‘yan jaridan kasar nan da iya sharrinsu.
“Kungiyarsu ta FCT ce ya kamata ta yi jagora ga sauran yankunan cikin kasar nan.
“Ba mu yi laifi ba idan muka zargi cewa wani ya biya kungiyar makudan kudade don ta bata mana suna.
“Bai kamata mu koya wa FCT NUJ aikin yi ba, amma ya kamata su dinga tabbatar da abu kafin su yi zargin wani akan laifi. Wannan abu da suka yi sun yi ne bisa ganganci don kawo cece-kuce,” kamar yadda takardar tazo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng