Sabuwar shekara na dauke da juna biyun abubuwa masu kyau ga yan Najeriya, gwamna Masari

Sabuwar shekara na dauke da juna biyun abubuwa masu kyau ga yan Najeriya, gwamna Masari

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, yace burikan yan Najeriya za su cika a sabuwar shekarar da aka shiga
  • Masari yace 2022 ce shekarar karshe ga shugaban kasa da wasu gwamnoni, don haka za su tabbatar sun inganta rayuwar yan ƙasa
  • Ya kuma ba da tabbacin cewa a bangarensa, gwamnatinsa zata fita da baki ɗaya karfinta wajen tabbatar da tsaro a Katsina

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya roki yan Najeriya su tsammaci zuwan abubuwa masu kyau gare su a sabuwar shekara 2022.

Daily Trust ta rahoto Gwamnan yace wannan shekarar da muka shiga tana ɗauke da juna biyun abubuwan alkhairi da damarmaki ga yan Najeriya

Aminu Masari ya yi wannan kyakkyawan fatan ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa ta bangaren yaɗa labarai, Abdu Labaran Malumfashi.

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali sai jam'iyyar PDP ta samu nasara a babban zaben 2023, Gwamna

Gwamna Masari na jihar Katsina
Sabuwar shekara na dauke da juna biyun abubuwa masu kyau ga yan Najeriya, gwamna Masari Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da yake bayyana hangensa mai kyau ga yan Najeeiya a 2022, Masari yace kasancewar wannan ce cikakkiyar shekarar ta ƙarshe ga shugaba Buhari da wasu gwamnoni, za su tabbata sun yi amfani da ita.

A cewarsa, shugaban ƙasa da wasu gwamnonin za su kara zage dantse a 2022 wajen kokarin da suke na inganta rayuwar yan Najeriya.

Gwamnati zata fuskanci abubuwa gadan-gadan

Masari ya tabbatar wa yan Najeriya cewa gwamnati zata fuskanci yaki da matsalar tsaro gadan-gadan, wanda zai hana yan ta'adda sakat.

Masari yace:

"Kalubalen da annobar korona da ayyukan yan bindiga suka jefa yan Najeriya abin damuwa ne, amma da izinin Allah gwamnatin mu zata fita da dukkan karfinta wurin tabbatar da kawo karshen rashin tsaro a 2022."

Fatan yan Najeriya zai cika a 2022

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Ya kuma ƙara da cewa abubuwan da yan Najeriya ke tsammani, da sannu za su same su, musamman game da lamarin matsalar tsaro.

Daga karshe Masari ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da baiwa gwamnati haɗin kai da goyon baya, musamman a wannan shekarar domin hakan zai taimaka wajen samu nasarori.

A wani labarin kuma Gwamnan PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace Allah ba zai gafarta wa PDP ba matukar jam'iyyar ta sake watsi da kiran yan Najeriya game da wanda suke so.

Wike yace yan Najeriya daga kowane sashi na kira ga PDP ta tsayar da gwamna Bala Muhammed na Bauchi a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262