Da zafi-zafi: Ganduje ya yi martani mai zafi ga Kwankwaso kan zargin murde zaben 2019
- Gwamnantin Kano ta yi martani mai zafi kan yadda Kwankwaso ya zargi Ganduje da murde zaben 2019
- Gwamnatin Ganduje ta ce kamata yayi Kwankwaso ya yabawa Ganduje bisa cika wasu ayyukan da ya bari
- Hakazalika, gwamnatin ta kuma ce bai kamata Kwankwaso ya zama mai maganganu irin wadannan ba
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi kaca-kaca da maganar murdiya da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben gwamna a 2019 ba, Daily Nigerian ta rahoto kawai ya yi makudi ne.
A makon nan ne aka samu wata hira da Ganduje yayi da wata gidan jaridar kasar nan, inda ya yi bayanai kan batutuwan da suka shafi zaben 2019 da ya gabata.
Cece-kucen da aka samu na zuwa ne kwana guda bayan da Ganduje ya yi tsokaci, a cikin sakonsa na sabuwar shekara, kan sasantawa da ubangidan nasa Kwankwaso.
Martanin Ganduje ya zo ne cikin wata sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar Muhammad Garba, ya fitar.
Sanarwar ta ce sabanin ikirarin Kwankwaso, tsohon gwamnan ya jagoranci wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, galibi da ba su da ko katin zabe suka shiga layin kada kuri'a.
Ya ce komai balo-balo yake cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a aka ce da yawan akwatunan zabe an cika su, daga baya INEC ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba.
Hakazalika, ya zargi cewa, ba tantance masu kada kuri'u ba don haka dole ne ma hukumar ta INEC ta soke sakamakon zabe daga cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba.
Ya kuma yi bayanin cewa, abin takaici ne yadda Kwankwaso a matsayinsa na jagoran a zaben, har yanzu yake magana kan sakamakon zaben da hukumomi suka gudanar kuma kotu ta amince da shi.
Kwankwaso ya nemi mabiyansa su kame bakinsu
A ci gaba da bayaninsa, Garba ya ce ba dadewwa ba Kwankwaso ya fito kafafen yada labarai ya gargadi mabiyansa kan tofa kalaman da basu dace ba amma sai ya gashi da kansa fadin irinsu.
Bisa ga dukkan alamu, a cewar kwamishinan, Kwankwaso ya yi yunkurin bata gwamnatin Ganduje da cewa ta yi masa illa fiye da alheri.
Ya kuma kara da cewa, bayanan Kwankwaso sun saba da da'awar samar da zaman lafiyar siyasar Kano da sulhu da ya lasa wa mabiyansa a ‘yan kwanakin nan.
Ya kamata Kwankwaso ya yabawa Ganduje
Garba ya kuma kara da bayyana cewa, kamata ya yi Kwankwaso ya gode wa Ganduje bisa kammala ayyukan da ya yi watsi da su kafin ya sauka a mulki.
Ya kuma kara da cewa al’ummar Kano sun ci gajiyar tsarin Ganduje na ci gaba da ayyukan da aka bari tare da kammala su cikin shekaru shida a jihar.
A Shirye na ke in yi sulhu da sanata Kwankwaso
A wani labarin, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya ce a shirye ya ke da ya gyara alakar da ke tsakaninsu da sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Daily Trust ta ruwaito.
A wata tattaunawa wacce Radio France ta yi da gwamnan ya kwatanta rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu da Kwankwaso tsakanin sabani.
Kamar yadda ya ce: “Kun san akwai masu hura wa rigima wuta. Don haka yanzu haka muna kokarin ganin mun dakatar da su tare da gyara alakarmu.
Asali: Legit.ng