Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da matar ɗan uwan kwamishina da ɗansu

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da matar ɗan uwan kwamishina da ɗansu

  • Wasu yan bindiga sun shiga gidan kanin kwamishinan muhalli na jihar Enugu, sun yi awon gaba da matarsa da kuma ɗansa
  • Rahoto ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da yan ta'adda suka shiga har gida suka sace mutane a yankin Eha-Amufu, Enugu
  • A halin yanzun mutane na cikin dar-dar domin ba su san abin da ka iya biyo wa baya ba daga jami'an tsaro

Enugu - Yan bindiga sun sace mata da ɗan Mista Eugene Edeoga, ƙanin kwamishinan muhalli na jihar Enugu, Chijioke Edeoga, ranar Asabar da daddare.

Punch ta rahoto cewa maharan sun sace su a cikin gidansu dake tsohuwar kasuwa a Eha-Amufu, karamar hukumar Isi-Uzo, jihar Enugu.

Wani shugaban al'umma a yankin, Chief Godswill Ndukwe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, yace tawagar jami'an tsaro bisa jagorancin yan sanda sun bazama domin ceto waɗan da aka sace.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sun yi awon gaba da matan aure da yan mata a sabon harin jihar Kaduna

Yan bindiga
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da matar ɗan uwan kwamishina da ɗansa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ndukwe, wanda yace ya samu rahoton lamarin da karfe 8:00 na safe, ya koka da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A halin yanzu Eha-Amufu ya shiga cikin tashin hankali tun bayan samun labarin sace waɗan nan mutanen ranar Asabar da yamma. Abun takaicin shine har gida aka je aka sace su."
"Wannan shi ne karo ba biyu da yan bindiga ke shiga har gida su sace mutane. Na farko shi ne sace ɗiyar shugaban yankin Agu-Amede a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Wane mataki yan sanda ke ɗauka?

Wani shugaban al'umma a yankin, Sunday Sharia, yace bayan sace mutane a makon da ya gabata, yan sanda sun shiga Eha-Amufu inda suka kame matasa.

A cewarsa tawagar yan sanda ta kame matasan, sannan ta laƙaba musu zargin suna da hannu da sace-sacen mutanen dake faruwa.

"A halin yanzun mafi yawansu na hannun yan sanda, yayin da aka sake sace wasu yanzu, to waye ke da hannu a wannan kuma?"

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa mutane sun kasa sukuni a Eha-Amufu bayan wannan lamarin sakamakon abin da yan sanda suka yi makon da ya gabata.

Kazalika da aka nemi jin ta bakin kakakin hukumar yan sanda reshen jihar, Daniel Ndukwe, bai ɗaga kiran waya ba kuma bai tura amsar sakonnin da aka tura masa ba

A wani labarin na daban kuma CAS ya roki dakarun soji dake karkashinsa su cigaba da luguden wuta har sai sun kammala aika yan bindiga lahira

Shugaban rundunar sojijin sama, Oladayo Amao, yace sojoji ba zasu kakkauta da hare-haren da suke kaiwa yan bindiga ba har sai sun karar da su baki ɗaya.

Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa taimakon da yake baiwa rundunar ta kowane ɓangare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262