Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya
- Basaraken Olubadan na kasar Ibadan, Olu Saliu Adetunji ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda rahotanni suka tattaro
- Majiyoyi daga masarautar sun tabbatar da rasuwar basaraken, duk da cewa a hukumance ba a bayyana hakan ba
- Marigayi Oba Saliu Adetunji ya hau karagar sarautar Ibadan ne a shekarar 2017 bayan rasuwar mahaifinsa
Ibadan, Oyo - Allah ya yi wa Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji rasuwa.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.
Jaridar Punch ta tattaro cewa sarkin ya rasu ne a asibitin kwalejin jami’a dake Ibadan a jihar Oyo.
Majiyoyin fadar sun tabbatar da mutuwarsa, amma sun nemi a sakaya sunayensu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da haka, da aka tuntubi, mataimakan sarkin ba su tabbatar da mutuwarsa ba kuma ba su musanta ba.
A cewar wani hadimin sarkin da aka zanta dashi ta wayar tarho:
“Ko da ya mutu, gwamna ne zai sanar da hakan."
Wani hadimin ya ce:
"Ba a jin labari mara kyau daga wurin malami."
Kokarin jin ta bakin Taiwo Adisa, mai taimaka wa gwamnan jihar Oyo kan harkokin yada labarai Seyi Makinde, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Adetunji, wanda ya karbi sarautar Olubadan na 41 a ranar 4 ga Maris, 2016, an haife shi ne a ranar 26 ga Agusta, 1928, kamar yadda This Day ta rahoto.
Shi ne na farko a cikin 'ya'yan iyayensa 17.
Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, basaraken garjiya mai sarautar Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III, ya rasu.
Majiyoyi na kusa da sarkin a fadar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa, basaraken mai shekaru 95 ya rasu ne da safiyar yau Lahadi.
Wasu majiyoyi guda biyu ne suka tabbatar da hakan a garin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng