A sakon sabuwar shekara, Ganduje ya yi magana kan sasanci da Kwankwaso da tsagin Shekarau
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi magana kan sasancin da yake so su yi da Sanata Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau
- A sakon sabuwar shekara da kwamishinan yada labarai na jihar ya fitar, ya ce gwamnan zai ba da fifiko wurin sasanci da bangarorin siyasa na jihar
- A cewar Ganduje, zai tabbatar da cewa zaman lafiya tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki na siyasa a jihar ya dawo domin cigaban al'umma
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya magantu kan bukatarsa na sasantawa da abokin hamayyarsa, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da tsagin APC karkashin shugabancin Sanata Ibrahim Shekarau.
A sakon sabuwar shekara, wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba yasa hannu a ranar Juma'a, Ganduje ya ce zai sadaukar da sabuwar shekarar wurin tabbatar da sabon tsarin zaman lafiya da sasanci tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyun siyasa a jihar da kasar baki daya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, duk da gwamnan bai kira sunayen 'yan siyasan ba, takardar ta jaddada bukatar shugabannin kungiyoyin siyasa na jihar da su hada kai domin kawo sabon tsari a siyasar jihar.
Ya ce:
"A yayin da aka ga manyan 'yan siyasar Kano suna jaddada bukatar sasanci, hakan ya sa jama'ar Kano fadawa farin ciki wadanda suke bukatar zaman lafiya da sasanci domin hakan ya kawo cigaba a siyasa da al'umma baki daya."
A cikin takardar, an tattauna kan yadda rashin tsaro ya tsananta a fadin kasar nan da kuma yadda talauci ya samu wurin zama a kasar nan.
Ya bayyana cewa, akwai tabbacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na kokari wurin shawo kan matsalolin da suka addabi kasar nan.
Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da magabacinsa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sun hadu bayan shekara da shekaru. Tsaffin abokan siyasan sun hadu ne a sashen VIP na tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja, DailyNigerian ta ruwaito.
Sun zauna dakin ne yayinda suke shirin hawa jirgi don zuwa jihar Kano. Jagororin biyu sun dade suna wasan buya tun lokacin da suka samu sabani bayan zaben 2015.
Asali: Legit.ng