Buhari ya nada Karebo Samson a matsayin mukaddashin kwanturola Janar na hukumar kashe gobara
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Karebo Samson a matsayin sabon kwanturola janar na hukumar kashe gobara ta tarayya
- Kakakin hukumar, DF Ugo Huan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 30 ga watan Disamba
- Yayin da yake jawabi a bikin karbar aiki a hedkwatar hukumar, Karebo ya yi godiya ga shugaban kasar kan wannan dama da ya bashi
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mataimakin kwanturola janar (DCG) Karebo Samson a matsayin sabon kwanturola janar na hukumar kashe gobara ta tarayya.
Kakakin hukumar, DF Ugo Huan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yammacin Alhamis, 30 ga watan Disamba, Daily Trust ta rahoto.
A cewar sanarwar, mukaddashin CG Karebo, yayin da yake jawabi a bikin karbar aiki a hedkwatar hukumar, ya yi godiya ga shugaban kasar kan wannan dama da ya bashi.
Mukaddashin CG Karebo ya yi alkawarin tabbatar da ganin cewa Jami’an sashin kula da ayyuka sun isar da aikinsu yadda ya kamata.
Yayin da yake kira ga Jami’an hukumar kashe gobarar da su zamo masu da’a, ya basu tabbacin cewa zai yi aiki da kowa don ciyar da hukumar gaba.
Kwanturola janar mai barin gado, Dr Liman Ibrahim, ya bukaci mukkadashin CG din da ya kammala duk wasu ayyuka da ke gudana a hukumar, rahoton The Cable.
Dr Ibrahim ya yi godiya ga Shugaban kasar a kan damar da ya basa na hidimtawa kasa. Ya ce gwamnati mai ci ta daga martabar hukumar daga halin tausayawa zuwa mai daraja.
Ya ce ba don hangen nesan shugaban kasar na kare rayuka da kayayyakin yan Najeriya ba, da hukumar kashe gobarar bata samu nasarorin da ta samu a karkashinsa ba.
Ya yi kira ga jami’an hukumar da su ba mukaddashin CG din cikakken goyon baya don samun nasara.
Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kuɗaɗen da aka sace, babu sisin kwabo da za mu ƙyalle, Buhari
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kwabon da zai yi kuka, bayan kammala binciken kudaden Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta, NDDC, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasar ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabi ta yanar gizo a taron kaddamarwar samfurin dakunan NDDC a jami’ar Uyo da ke Akwa Ibom.
Buhari ya ce an kammala kididdigar kuma an gano inda ko wanne kwabo ya sake yayin da ko wanne mai laifi zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.
Asali: Legit.ng