Shugaba Buhari ya yi ta’aziyar mutuwar tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad
- Buhari ya bayyana marigayin a mutum mai tarin sani wanda ya yi wa al'umman hidima
- Ya ce ba za a taba mantawa da koyarwarsa da gudunmawar da ya bayar wajen kyautata rayuwar al’umma ba
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jana’izar kwararren likitan mafitsara kuma jagoran cibiyar kiwon lafiya mai zaman kanta a Kano, Dr. Ibrahim Datti Ahmed.
Shugaban kasar, a sakon ta’aziyyar marigayi likitan kuma dan siyasa wanda ya taba takarar kujerar shugaban kasa, ya bayyana shi a matsayin mutum mai tarin sani.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya fitar da sakon ta’aziyyar a yau Alhamis, 30 ga watan Disamba, Daily Trust ta rahoto.
Buhari ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Dr. Datti ya kasance kan gaba wajen samar da kiwon lafiya ga talaka da mabukata. Ba za a taba mantawa da koyarwarsa da gudunmawar da ya bayar wajen kyautata rayuwar al’umma ba. Za a dunga tunawa da shi kan hidimar da yayi wa al’umma.”
Shugaban kasar ya ce kasar na tare da iyalan marigayin, majalisar masarautar Kano da gwamnati da mutanen jihar yayin da suke juyayin rashin likitan, dan siyasa kuma Shugaban addini, rahoton The Sun.
Marigayi Dr Ahmed, wanda ya kasance abokin marigayi shugaban kasa Murtala Mohammed, ya kasance wanda ya kafa asibitin Asmau Memorial Hospital, wanda aka sauya wa suna zuwa Abubakar Imam Urology Centre a Kano.
Haka kuma ya yi aiki a matsayin shugaban majalisar shari’a ta Najeriya.
Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa
A baya mun kawo cewa Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ahmad, rasuwa ranar Alhamis a jihar Kano.
Legit ta tattaro cewa Dr Datti ya rasu ne bayan rashin lafiya da yayi fama.
Diraktan tashar Sunna TV, Dr Abu Aisha Ibrahim Disina a jawabin ta'aziyyarsa ya bayyana cewa za'a yi Sallar jana'iza a Masallacin Al-Furqan dake Kano misalin karfe 10 na safe.
Asali: Legit.ng