‘Yan Sanda sun tabbatar da kisan Basarake da cafke wani yaron Bello Turji a jihar Zamfara

‘Yan Sanda sun tabbatar da kisan Basarake da cafke wani yaron Bello Turji a jihar Zamfara

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen Zamfara sun tabbatar da harin da aka kai a garin Bungudu
  • Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, Ayuba Elkanah yace an kashe Hakimin Gada, Umaru Bawan-Allah
  • Dakarun ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun cafke wani ‘Dan bindiga ya na shirin garkuwa da mutane

Zamfara - Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Zamfara, sun tabbatar da mutuwar Hakimin Gada a kasar Bungudu, jihar Zamfara, Alhaji Umaru Bawan-Allah.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami’an tsaro sun bada sanarwar cewa Alhaji Umaru Bawan-Allah da wasu mutane hudu sun mutu a harin ‘yan bindiga.

Baya ga haka, ‘yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar cafke wasu mutane da ake zargin su na cikin ‘yan bindigan da suka addabi mutane a kauyukan jihar.

Kara karanta wannan

An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa

Sannan an ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su, an kuma karbe wasu manyan makamai.

Kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara, Ayuba Elkanah ya bayyana wannan a yayin da ya yi hira da manema labarai a Gusau a ranar 29 ga watan Disamba, 2021.

‘Yan Sanda
Wasu Dakarun 'Yan Sandan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin kwamishinan 'yan sanda

“A yau (ranar Laraba) da kimanin karfe 3:35 na rana, ‘yan bindiga suka dura kauyen Gada, a karamar hukumar Bungudu, inda suka kashe Hakimin garin, Umaru Bawan-Allah da wasu mutum hudu, kuma suka yi garkuwa da jama’an yankin.”
“Jami’an ‘yan sanda da dakarun sojoji da ‘yan sa-kai, sun yi maza sun shiga aiki, suka yi ta musayar wuta da ‘yan bindigan a wani gumurzu da aka yi.”
“Dakarun hadin-gwiwar sun yi nasarar kora ‘yan bindigan, suka ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su, daga ciki har da ‘dan jariri mai shekara daya.”

Kara karanta wannan

Zamfara: Mutane sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 10 sun sace mata 33

“Abubuwa sun dawo dai tuni, a dalilin kokarin da jami’an tsaro suke yi.” - CP Ayuba Elkanah.

An kama Mai 'yan mata - CP Ayuba Elkanah

A jawabin da ya yi wa ‘yan jarida, Ayuba Elkanah yace a ranar Talata ‘yan sanda suka yi nasarar cafke wani hatsabibin dan bindiga mai suna Mai ‘yammata.

PM News ta ce shu'umin ya shiga hannu ne ya na kokarin tare titi, ya dauke mutane a kauyen Koliya. ‘Dan bindigan ya na cikin tsofaffin yaran Bello Turji.

Yanzu wannan 'dan bindiga ya na aiki ne da Kachalla Sani-Black. An samu AK-47, harsasu da babur a hannunsa. Idan an gama bincike, za a kai shi kotu.

An dauke Sarkin kasar Gindiri

A jiya ne aka ji labarin yadda wasu miyagun ‘Yan bindiga su ka je har gidan Sarkin kasar Gindiri, su ka yi awon gaba da shi cikin tsakar dare a ranar Talatar nan.

Kara karanta wannan

Babu kanta yayin da ‘Yan bindiga suka dauke Mai daki, 'ya ‘yan ‘Dan Sanda a jajibirin Kirismeti

Wani 'dan uwan Basaraken yake cewa ‘yan bindigan sun shafe kusan sa’a guda kafin su iya shiga gidan Sarkin Mangu, a karshe suka yi nasarar yin gaba da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel