Ku cigaba da ruwan wuta har sai kun aika baki daya yan bindiga lahira, CAS ya roki sojoji

Ku cigaba da ruwan wuta har sai kun aika baki daya yan bindiga lahira, CAS ya roki sojoji

  • Shugaban sojin sama NAF, Oladayo Amao, ya umarci dakarun sojoji su cigaba da kaddamar da hare-hare kan yan bindiga a sassan ƙasar nan
  • Amao ya bukaci sojojin kada su sassauta daga luguden wuta har sai sun kammala aika yan bindiga baki ɗaya lahira
  • Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa taimakon da yake baiwa rundunar ta kowane ɓangare

Minna, Niger - Shugaban rundunar sojin sama (NAF), Oladayo Amao, ya umarci dakarunsa su cigaba da ruwan wuta ba kakkautawa har sai sun ƙarar da yan bindiga baki ɗaya.

Kakakin NAF, Edward Gabkwet, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yace Amo ya bada wannan umarnin ne yayin da yake bikin kirsimeti tare da sojojin Operation Gama aiki da dakaraun runduna ta 013 a Minna, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun yi awon gaba da baban sarki a jihar Arewa

The Cable tace Amao, wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan Operations, yace ayyukan yan bindiga da yan ta'adda ya zama barazana ga cigaban ƙasa.

CAS Amao
Ku cigaba da ruwan wuta har sai kun aika baki daya yan bindiga lahira, CAS ya roki sojoji Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa haɗin guiwar da ake samu tsakanin hukumomin tsaro yana taimaka wa sosai wajen fuskantar wasu ƙalubalen dake damun kasar nan.

Premium Times ta rahoto Hafsan sojin yace:

"Ya zama wajibi na bayyana alfahari na da ku baki ɗaya, sojojin sama maza da mata, musamman waɗan da ke bada gudummuwa a aikin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan."

Amao ya jinjina wa shugaba Buhari

Da yake jero nasarorin da NAF ta samu, shugaban sojijin sama ya yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bisa dumbin goyon bayan da yake baiwa rundunar.

"Abun alfahari ne yadda NAF ta samu cigaba da karin karfi a baya-bayan nan, inda muka samu karin matukan jirgi 26 da kuma masu sarrafa jirage 31 tun bayan kama aiki na."

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

"Haka nan kuma ina farin cikin bayyana cewa a yanzu muna da adadin sojoji 195 maza da mata, dake kwas ɗin ɗaukar horo na musamman a kasashen waje."

Amao ya ƙara da cewa akwai wasu matukan jirgi dake makarantar daukar horo a Kano da sauran cigaban da hukumar sojin sama ke ƙara samu.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a sabon harin jihar Zamfara

Wasu miyagun yan bindiga sun kashe basarake a wani sabon hari da suka kai yankin masarautar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna kauyen Gada sun bayyana cewa maharan sun cinna wuta a motocin masarauta da kuma kayan abincin da suka taras.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262