Katsina: Za mu dage dokar dakile layikan sadarwa kafin watan Janairun, Masari
- Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dage dakatar da kafofin sadarwar da ta yi a kananun hukumomi 7 da lamarin ya shafa a watan Janairun 2022
- Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya bukaci mazaunan su yi iyakar kokarinsu akan kare kansu daga harin ‘yan bindiga
- Dama gwamnatin ta datse kafafan sadarwar ne don hana ‘yan bindiga tattaunawa da ‘yan uwansu yayin da jami’an tsaro su ke ayyukansu
Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dage dokar datse layikan sadarwar da ta yi a kananun hukumomi 7 da lamarin ya shafa a watan Janairun 2022, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar ya shaida hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a Katsina inda yace mazauna yankunan su kare kawunansu daga harin ‘yan bindiga.
Gwamnatin ta datse kafafen sadarwar ne don hana ‘yan bindiga damar tattaunawa da juna yayin da jami’an tsaro su ke yin ayyukansu a jihar.
Sai dai gwamnatin bata dade da dage dokar ba a kananun hukumomi 10 cikin 17 din da su ka fuskanci hare-haren.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yaba da kokarin jami’an tsaro musamman ‘yan sa kai akan yaki da ta’addanci.
Masari ya kula da yadda ‘yan sa kan su ka dinga zuwa kare garuruwa daga hare-haren, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya shawarci jama’a akan ba jami’an tsaro hadin kai musamman muhimman bayanai akan ‘yan ta’addan.
Har ila yau, gwamnan ya hori mutanen garuruwan da abin ya shafa da su ba wa ‘yan sa kai cikakken hadin kai da kuma makamai don kawo karshen ta’addanci a jihar.
Gwamnati ta buɗe hanyoyin sadarwa da aka datse a jihar Katsina
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta sanar da dawo da amfani da layukan sadarwa a sassan jihar.
Rahoton Aminiya Hausa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dawo da sabis da ta datse a baya a yunkurin dakile yawaitar ayyukan yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Gwamnati ta ɗauki matakin datse hanyoyin sadarwa da wasu matakai ne a wasu kananan hukumomin jihar domin yaki da ta'addancin yan bindigan daji.
Asali: Legit.ng