Magidanci ɗan shekaru 80 ya kashe matarsa don ta fasa kwanciyar aure da shi bayan ya sha maganin ƙarfin maza
- Wani magidanci dan kasar Italy mai shekaru 80, Vito Cagani, ya halaka matarsa, Kyrychok, mai shekaru 61 ta hanyar caka mata wuka
- Cagani ya halaka matarsa ne a lokacin kirsimeti saboda ta yi alkawarin za su yi kwanciya irin ta ma'aurata amma ta fasa bayan ya sha maganin karfin maza
- Bayan ya halaka ta, mijin, Cagani ya kira mai gidan matarsa a wurin aiki ya fada masa cewa ya san suna soyayya kuma ba zai ake ganinta ba
Italy - Wani mutum mai shekaru 80, Vito Cagani, ya daba wa matarsa, Kyrychok, wuka a a ranar Kirsimeti bayan ta yi alkawarin za su yi kwanciyar aure amma ba canja ra'ayinta, PM News ta ruwaito.
Mutumin ya sha maganin kara karfin maza a yayin da ya zauna yana jiran ta a gidansa da ke Fanano di Gradara a gabashin Italy.
Rashin amincewar da ta yi masa yasa ya fusata shi, inda ya yi zargin tana soyayya da mai gidanta awurin aiki. Ma'auratan sun shafe kimanin shekaru 20 suna tare.
Mutumin, bayan caka wa matarsa mai shekaru 61 wuka har sau hudu har ma a zuciyarta, ya bar ta kwance cikin jini a kasa yayin da shi kuma ya hau gado ya yi kwanciyarsa, Daily Mail ta ruwaito.
Kamr yadda rahotani suka bayyana, bayan gari ya waye, ya yi karin kumallo, sannan ya fita da karensa waje suka yi tattaki suka dawo gida tamkar ba abin da ya faru.
Sannan sai ya kira mai gidan matarsa na wurin aiki a wayar tarho ya fada masa cewa ba zai sake ganin Kyrychok ba.
Cangini ya fada wa mai gidan matarsa cewa:
"Na san akwai abin da ke faruwa a tsakanin ku."
Mai gidan matar ya sanar da yan sanda
Mutumin, wanda ke da wurin cin abinci ya kira yan sanda, sannan suka ziyarci gidan wacce abin da ya faru da ita. Jami'an sun tsinci gawar Kyrcychok a kasa da raunin wuka a kalla guda hudu, har a zuciya.
Nan take aka kama Cangini aka tsare shi, an kuma gano makamin da ake zargin an aikata kisar da shi a gidan.
A halin yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin.
Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.
A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.
Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.
Asali: Legit.ng