Na warke daga cutar COVID-19, Kakakin Buhari, Garba Shehu

Na warke daga cutar COVID-19, Kakakin Buhari, Garba Shehu

  • Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu ya ce ya warke daga cutar COVID-19 da aka fi sani da korona
  • Garba ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook a ranar Laraba 29 ga watan Disamba
  • Kakakin shugaban kasar ya mika godiya ta musamman ga wadanda suka taya shi da addu'oi tare da kiransa ko tura masa sakon samun sauki

FCT, Abuja - Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan watsa labarai, Malam Garba Shehu, a ranar Laraba ya ce ya warke daga cutar COVID-19 wato korona da ta kama shi.

Shehu na cikin hadiman shugaban kasa da suka kamu da cutar a cikin makon da ta gabata.

Na warke daga cutar COVID-19, Kakakin Buhari, Garba Shehu
Kakakin Buhari, Garba Shehu ya ce ya warke daga korona. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shehu, cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce:

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hadimin Buhari, Garba Shehu ya warke daga cutar Korona

"Ina mika godiya ga Allah madaukaki da ya bani sauki cikin gaggawa daga cutar COVID-19.
"Ina addu'a da matukar godiya ga dukkan wadanda suka taya ni da addu'a, suka turo sako ko kuma suka kira domin nuna damuwarsu a gare ni.
"Da fatan dukkan yan kasarmu da suka kamu da cutar za su yaki kwayar cutar da dukkan karfinsu sannan su samu sauki cikin gaggawa."

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

A wani bangare na kokarin ganin an kiyaye dokar lafiya, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da haramtawa wuraren shakatawa da bukukuwa da majami’u na addini da ke da mabiya sama da 50 yin taro.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun shiga gidaje, sun hallaka hakimi da wasu mutane a jihar Zamfara

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga Disamba, ta ce an sanar da matakin ne sakamakon sake barkewar Korona.

Hakazalika, gwamnati ta ce gazawar mazauna Abuja wajen daukar matakan kariya masu sauki abin damuwa ne ga lafiyar al'umma.

Gwamnatin, a cikin wata sanarwa da Sakataren, Sakateriyar Lafiya da Ayyukan Jama’a Dr. Abubakar Tafida ya fitar, ta yi kira ga mazauna Abuja da su dauki matakin kare kansu da ‘yan uwansu daga wannan annoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164