Kwana 12 da rasuwar tsohon Shugaban Majalisa, Matar da ke yi masa takaba ta bi shi barzahu
- Mary Abiola Wayas ta mutu kwanaki kadan bayan mai gidanta, Joseph Wayas ya riga mu gidan gaskiya
- Kamar dai mijin na ta, ita ma Mary Abiola Wayas ta rasu ne a kasar waje bayan tayi ta 'yar rashin lafiya
- Joseph Wayas Jnr ya bada sanarwar mutuwar, yace sun rasa mahaifiyarsu kwana 12 da rasuwar mahaifi
Miss Mary Abiola Wayas, mai dakin marigayi Sanata Joseph Wayas ta riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni daga jaridar The Eagle sun tabbatar da cewa Mary Abiola Wayas ta rasu ne a wani asibiti a kasar Birtaniya.
Mutuwar Mary Abiola Wayas ya zo kwanaki 12 da rasuwar mai gidanta, Joseph Wayas wanda ya rasu a watan Nuwamba.
Joseph Wayas Jnr yace mahaifinsu ya rasu ne a wani asibiti a kasar Turai a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2021.
Ita kuwa mahaifiyar ta su ta mutu a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, 2021, bayan tayi fama da gajerar rashin lafiya.
Wacece Mary Abiola Wayas?
A wani rahoto da jaridar The Will ta fitar, an ji cewa Mary Abiola Wayas ta mutu ta bar ‘ya ‘ya biyar da suke raye.
Baya ga haka, tsohuwar kwararriyar sakatariyar ta bar jikoki da wasu tattaba-kunne da-dama.
Mary Wayas ta yi aiki a manyan kamfanonin Duniya a Russell Square, Landan, a lokacin mai gidanta na karatu a Ingila.
Marigayiyar ce ta rika taimakawa Joseph Wayas a makaranta kafin ya zama abin da ya zama.
Bayan dawowarsu gida, Wayas ya shiga siyasa, har ya zama shugaban majalisar dattawa tsakanin 1979 da 1983.
Rahoton ya bayyana cewa wannan Baiwar Allah ta bar Duniya ta na da shekaru 78 da haihuwa.
Halaccin gwamnan Benuwai
An ji cewa Gwamnan Benuwai Samuel Ortom ya yi sakayya ga direban da ya ba shi aikin yaron mota shekaru sama da 40 da suka wuce.
Ortom ya ba Mnenge Mtemave sabuwar mota, ya kuma yi alkawarin taimaka masa da kasuwanci, sannan ya ba abokan aikinsa kyauta.
Asali: Legit.ng