Obasanjo ga Clark: Niger Delta ba ta isa ta nuna iko kan man fetur din Najeriya ba

Obasanjo ga Clark: Niger Delta ba ta isa ta nuna iko kan man fetur din Najeriya ba

  • Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya ce yankin Niger Delta ba ta da hurumin ikirarin mallakar man fetur din Najeriya
  • Tsohon shugaban kasar Najeriya ya ce duk wasu ma'adanai da ke kasar nan a kowanne yanki, mallakin Najeriya ne ba yankin ba
  • Obasanjo ya yi kira ga Edwin Clark da ya kasance dattijon kasa ba kabilarsa ba, hakan ne zai sa ya zama dan kasa nagari

Ogun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce dukkan man fetur da ke yankin Niger Delta na Najeriya ne kuma yankin bai isa ya nuna iko kan fetur ba matukar suna cikin Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Obasanjo ya ce kowanne ma'adanai da ke kowanne bangare na kasar nan mallakin kasar ne ba na yankin ba.

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

Obasanjo ga Clark: Niger Delta ba ta isa ta nuna iko kan man fetur din Najeriya ba
Obasanjo ga Clark: Niger Delta ba ta isa ta nuna iko kan man fetur din Najeriya ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya sanar da hakan ne yayin martani ga fitaccen shugaban kabilar Ijaw, Edwin Clark, wanda ya zargi cewa Obasanjo ya tsani yankin Niger Delta.

Obasanjo ya ce Najeriya da yankin Niger Delta suna tsammanin Clark ya kasance dattijon kasa ba dattijon kabila ba, Daily Trust ta ruwaito.

Clark mai shekaru 94 shi ne shugaban kungiyar 'yan Niger Delta kuma shugaban kungiyar yardaddun Ijaw na kasa.

Ya yi aiki a matsayin kwamishinan yada labarai na tarayya a 1975 kuma ya kasance cikin siyasa tun kafin samun 'yancin kan Najeriya.

Obasanjo mai shekaru 84, a doguwar wasikar da yayi wa Clark, ya ja kunnen shugaban Ijaw kan yin amfani da miyagun kalamai wurin kwatanta shi.

Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis ya koka akan yadda yaran da suka daina zuwa makaranta za su koma ‘yan kungiyar Boko Haram.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin jawabi a wani taron gogar da matasa akan mulki a cibiyar ci gaban matasa da ke Olusegun Obasanjo Library, Abeokuta, jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi nuni akan yadda kusan dalibai miliyan 14 suka daina zuwa makarantu su na yawo a titinan Najeriya, inda ya ce ba sai an fada wa kowa ba, ya san nan da shekaru 10 zasu zama ‘yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng