Ba mu amince ba: Ƙungiyoyin arewa suna shirin yin gagarumin zanga-zanga kan ƙarin ƙudin man fetur
- Kungiyar arewa ta soki matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur a 2022, ta yi barazanar ba za ta amince ba
- Kungiyar ta kuma yi martani kan alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi na maye gurbin tallafin da N5,000 da za a rika bawa yan Najeriya miliyan 40
- Matakin na gwamnatin tarayya na janye tallafin man fetur da kara kudin man zuwa N340 duk lita na cigaba da daukan hankalin mutane a kasar
Jihar Kano - Gamayyar kungiyoyin arewa, CNG, na yankin kudu maso kudu ta nuna kin amincewarta da shirin karin kudin man fetur da gwamnatin tarayyar Najeriya ke yi.
The Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta yi barazanar yin zanga-zanga idan har gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da shirin ta na janye tallafin man fetur ba a 2022, .
Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta, Alhaji Yakubu Aliyu, wanda ya raba wa manema labarai, ranar Litinin 27 ga watan Disamba a Kano.
Kungiyar ta kuma kara da cewa alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi na maye gurbin tallafin man fetur da N5,000 da za ta rika bawa mutane miliyan 40 a kasar ba abu bane mai yiwuwa domin ba zai yi maganin wahalhalun da karin kudin man zai janyo ba.
Wani sashi na sanarwar ya ce:
"Gammayar kungiyoyin arewa yankin kudu maso kudu tana nuna rashin amincewarta da karin kudin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi kan farashin man da a yanzu ma ke da tsada.
"Idan har gwamnati ba ta ji gargadin mu ba, kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin fara zanga-zanga don nuna rashin amincewarta da karin.
"Abin da ya fi damuwa kuma shine tsarin da gwamnatin za ta fito da shi na bawa tsirarun miliyoyin yan Najeriya N5,000 duk wata don rage radadin karin farashin man fetur din, wanda ba a san iya hauhawar farashin kaya da zai haifar ba.
Ta cigaba da cewa:
"Bisa la'akari da wannan, kungiyar mu tana kira ga gwamnatin tarayya ta y watsi da wannan matakin da ba zai amfani talaka ba, domin tabbas zai tsananta halin matsin da mutane ke ciki ne."
Asali: Legit.ng