Sojoji sun yi kicibis da ‘Yan bindiga a asibiti, sun ki mutuwa a hare-haren da aka kai a Zamfara
- A makon da ya wuce ne Dakarun sojojin Najeriya suka yi barin wuta a sansanin ‘Yan bindiga a Zamfara
- An hallaka wasu ‘Yan bindigan da suka fake a sansanin Alhaji Zaki, Alhaji Mai daji da irinsu Kachalla Doso
- Sojoji sun hadu da wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka samu rauni, su na jinya a wani karamin asibiti
Zamfara - Jaridar PR Nigeria tace Dakarun sojojin Najeriya sun cafke wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su na jinya a wani asibiti a jihar Zamfara.
Rahoton ya bayyana cewa daga cikin wadanda sojojin su ka samu a asibitin akwai wasu ‘yan bindigan da suka kubuta daga luguden wutan dakaru.
Sojojin sama sun yi wa sansanin manyan ‘yan bindigan Zamfara irinsu Alhaji Zaki, Mai daji da Kachalla Doso a ranar Juma’ar da ta wuce barin wuta.
Rundunar sojojin sama na tawagar Operation Hadarin Daji sun yi kokarin tarwatsa ‘yan bindigan da suka addabi kauyukan Zamfara da makwabtansu.
An kai hari a Birnin Magaji
Wasu da-dama daga cikin ‘yan bindigan da suka fake a Shamushelle a garin Birnin Magaji sun mutu, sai dai kuma akwai wadanda suka sha da kyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoto daga majiya mai karfi yace wannan luguden wutan ya yi tasiri sosai a jejin Shamushelle.
Daily Nigerian ta ce harin sojojin saman ya durkusa miyagun ‘yan bindigan da ke tare da Alhaji Zaki, Alhaji Maidaji, Kachalla Doso da Kachalla Kariga.
Wasu miyagu sun sha da kyar
A cikin wadanda suka sha da kyar ne aka samu wadanda aka ji wa rauni, su na jinya a wani asibiti, yanzu sun sake fadawa hannun wasu jami’an tsaron.
“Jami’an tsaro sun yi ram da kusan ‘yan bindiga takwas da suka samu rauni, sun je wani karamin asibiti domin a kula da su.” - Majiyar.
Hakan na zuwa ne a lokacin da jami’an tsaro ke kokarin kawo karshen ‘yan bindigan da suke fake a dajin yankunan Zamfara da wasu bangarorin jihar Sokoto.
An ba kauyukan Zamfara wa'adi
A yau ne wa'adin da 'yan bindiga su ka bada zai cika, an nemi mutanen Bawagauga, Hayin Uda, Ruguza, Dumuyu, Zigau, Mai-Rerai da Gidan Kado su tara N37m.
'Yan bindiga sun tasa kauyukan karamar hukumar Tsafe a gaba, sun ce dole sai an ba su wadannan miliyoyin, idan ba haka ba kuma za su kai hare-hare.
Asali: Legit.ng