Yan Shi'a sun halarci bikin Kirismeti tare da mabiya addinin Kirista a Zaria

Yan Shi'a sun halarci bikin Kirismeti tare da mabiya addinin Kirista a Zaria

  • An yi murnar ranar Kirismeti a fadin duniya ranar Asabar, 25 ga watan Disamba, 2021
  • Limamin Coci a garin Zaria ya bayyana mamakinsa bisa yadda mabiya Shi'a suka kawo masa ziyarar cocinsa
  • Jagoran mabiya Shi'an yace sun hallara ne don watsi da duk wani rashin fahimta da aka cusa tsakanin Musulmai da Kirista

Zaria - Gomman mabiya akidar Shi'a sun halarci bikin Kirismeti a Cocin HEKAN dake garin Zariya jihar Kaduna ranar Asabar, 25 ga Disamba, 2021.

Shugaban Cocin, Hakila Darmah, wanda ya karbi bakuncinsu ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karamci, rahoton NAN.

Yace:

"Gaskiya na yi farin ciki sosai ganin yadda suka yi tunani irin wannan na kawo mana ziyara ranar murnar Kirismeti."

Darmah ya yi kira ga sauran yan Najeriya suyi koyi da yan Shi'a domin kara danko zumunci.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan Musulmai da suka halarci coci domin taya Kiristoci murnar Kirsimeti

Cocin mabiya addinin Kirista a Zaria
Yan Shi'a sun halarci bikin Kirismeti tare da mabiya addinin Kirista a Zaria Hoto: DN
Asali: Facebook

Shugaban yan Shi'an da ya suka kai ziyarar, Farfesa Isa Mshelgaru ya bayyanawa manema labarai cewa sun kai wannan ziyara ne domin raya soyayya, zaman lafiya da zamantakewa.

Yace:

"Mun yanke shawarar halartan wannan coci ne yau saboda yau Kirismeti, ranar haihuwar Yesu ne da ake murna a fadin duniya kuma muna ganin ya kamata mu tayasu murna."
"Yayinda Kiristoci suka dauki wannan rana da muhimmanci, shi yasa muka zo watsi da duk wani rashin fahimta da aka cusa tsakanin Musulmai da Kirista."

Kalli hotunan:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng