Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan ta'adda, yanki ne da ya dade yana nuna wariya ga mata da matasa. Bugu da kari, rashin aikin yi ya yi katutu a yankin hakan yasa matasa ke gararamba a gari suna aikata laifukan da ke kara dilmiya yankin cikin matsala.

Musamman, Jihar Kano tana fama da kallubalen isassun ayyukan yi ga dimbin matasa da ke jihar-mafi yawancinsu mata. Yayin da gwamnatin jihar na kokarin sauya lamarin, akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu musamman a yanzu.

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai
Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai
Asali: Facebook

Bisa la'akari da wannan kallubalen ne yasa gidauniyar Coca-Cola ta (TCCF), da ke yin ayyukan tallafawa al'umma ta kaddamar da 'Project EQUIP, wani shirin koyar da sana'o'i tare da hadin gwiwar kungiya mai tallafawa al'umma, Gidauniyar Whitefield.

An yi imanin cewa wannan shirin da kamfanin ta kaddamar zai taimakawa kimanin mata da matasa 20,000 a yankin da nufin kawar da matsalar da ke adabar yankin. Ga muhimman bangarorin da shirin zai mayar da hankali a kansu bayan kaddamar da shi a wannan watan:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn

1. Tallafawa mata

Saboda dalilai na kabilanci, al'ada da addini, mata a arewa su kan fuskanci wariya a mafi yawancin lokuta. Majalisar Dinkin Duniya, UN, ta yi ikirarin cewa mata da 'yan mata ne rabin al'ummar jihar amma ba su samun dama da za su bada irin gudunmawar da ya kamata a matsayinsu na masu kawo canji.

Alkalluma daga gwamnati ya yi kamanceceniya da wannan ikirarin na UNICEF inda ya nuna cewa 4 ne cikin mata 10 a arewa ke zuwa makaranta saboda dalilai da suka hada da talauci da rashin samun dama.

Saboda damuwa da wannan matsalar, wannan shirin da TCCF ta dauki nauyi zai mayar da hankali kan mata da ke jihar. Ta shirin Project EQUIP, za a tallafawa mata a Kano da sana'o'i, hakan zai karfafa su su rika tsayuwa da kansu.

2. Magance rashin tsaro

A farkon wannan shekarar, Strong Cities Network (SCN) ta yi tuntuba a jihohin arewa maso yamma da suka hada da Kano, Kaduna, Katsina da Zamfara. Binciken ya sa kungiyar ta fahimci matsalolin da tashin hankali ke kawo wa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga

A cewar kungiyar, daga aikin abubuwan da ke kawo tashin hankali akwai talauci da rashin ababen more rayuwa, duk da cewa wadanda aka tambaya sun ce gwamnati na kokarin magance matsalolin. Saura sun hada da rashin aikin yi ...

Rage tashin hankula na daga cikin muhimman abinda Project EQUIP ta sa a gaba. Duba da cewa dubban mutanen Kano za su amfana da shirin koyar da su sana'o'i da za su sauya rayuwarsu, ana fatan ganin canji a batun na tashe-tashen hankula.

3. Kawo cigaba mai dorewa

Tsarin rayuwa da wariya na cigaba da dakile wa mata damar fadin albarkacin bakinsu a kan batutuwan da suka shafe su a gidaje da unguwaninsu.

A cewar UN Women, tallafawa mata su tsaya da kansu yana bunkasa tattalin arziki da ingancin aiki da daidaito wurin samun kudaden kashewa da sauran cigaba masu amfani.

Bisa la'akari da wannan, hasashen da akalluma suka tabbatar da sahihancinsa, ba abin mamaki bane ganin yadda ake ware mata wurin batun tattauna tattalin arziki. Amma, Shirin Coca-Cola ta 'Project Equip' zai yi kokarin ganin mata suna bada gudunmawarsu don cigaban al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Da shirin Project Equip, Coca-Cola za ta cigaba da bada gudunmawa domin sauya rayuwar mutane ta hanyoyin da zai amfane su.

Masu sha'awa suna iya rajista a shirin a nan. Za a rufe rajista a ranar 31 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: