Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari yace gwamnatinsa ba zata sassauta wa yan bindiga ba, har sai ta ga bayan su musamman a arewa ta yamma
  • Buhari yace idan yan Najeriya za su yi wa gwamnatinsa adalci, yanayin da ya samu kasar da yanzun ba daya bane
  • Ya kuma kara tabbatar da cewa nan da watanni 17 idan wa'adin mulkinsa ya cika zai sauka ya miƙa wa wani

Borno - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata yi amfani da karfin soji wajen ragargazan yan bindigan da suka hana yan Najeriya zaman lafiya.

Dailytrust tace Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga al'ummar jihar Borno ranar Alhamis, a wata ziyarar aiki da ya kai jihar.

Kara karanta wannan

Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Ali Nuhu

Yayin ziyarar shugaba Buhari ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Borno da fitaccen ɗan kasuwan nan, Alhaji Muhammadu Indimi, suka yi.

Shugaba Buhari
Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari, wanda ya nuna tsantsar damuwarsa, yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina sane da nasarar da muka samu a nan, da kuma gazawar mu a wani ɓangaren, musamman yankin da na fito wato arewa maso yamma, inda zaka ga mutane masu al'ada ɗaya amma suna kashe juna, dan me?"
"Mun siyo kayan aiki wa sojoji daga ƙasar Amurka, jiragen yaki, jirgi mai saukar angulu, motocin yaki kuma sun fara iso wa, ba zamu sassauta wa yan bindiga ba."

An samu tsaro fiye da baya - Buhari

Buhari ya kara da cewa babbar matsalar dake faruwa a arewa ta yamma shi ne, mutanen nan kabila daya da al'ada ɗaya, amma sun hana yan uwansu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

"Idan yan Najeriya za su mana adalci, wane yanayi muka samu ƙasar nan, kuma wane hali take ciki a yanzu. Mutanen yankin arewa maso gabas sun fi kowa sanin halin da muka samu ƙasar nan."

Buhari ya kara ba da tabbacin cewa da zaran wa'adin mulkinsa ya kare nan da watanni 17 a shekarar 2023, zai sauka daga kan mulki.

A wani labarin kuma Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari

Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262