Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter
- Rahoton da muke samu ya bayyana irin makudan kudade da gwamnati ta yi asarar su saboda dakatar da Twitter
- A binciken da aka yi, gwamnati ta rasa akalla N499.32bn daga lokacin da aka dakatar da Twitter zuwa yanzu
- Masana sun bayyana ta yadda gwamnati ta rasa wadannan kudade, da kuma yadda masu kasuwanci suka jikkata ta dalilin dakatarwar
Abuja - Tattalin arzikin Najeriya ya yi asarar N499.32bn sakamakon rufe shafin Twitter tun daga ranar 4 ga Yuni, 2021.
A ranar 4 ga watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da Twitter bayan da kafar ta goge sakon da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, inji rahoton Punch.
A ranar 5 ga watan Yuni ne kamfanonin sadarwa suka hana 'yan Najeriya shiga Twitter bayan sun samu umarni daga hukumar sadarwa ta Najeriya kan haka.
A cewar NetBlocks Cost of Shutdown Tool, tattalin arzikin Najeriya na asarar N104.02m ($ 250,600) a kowace sa'a, saboda dakatar da Twitter. Sa'o'i 4,800 (kwana 200) kenan tun lokacin da aka toshe dandalin na sada zumunta.
Yayin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kai, Buhari ya yi nuni da cewa dokar za ta ci gaba har sai an yiwa Twitter rajista a Najeriya da dai sauran bukatun gwamnati.
Kwanan nan, Karamin Ministan Kwadago da Aikin yi, Festus Keyamo, ya ce Twitter ya amince da sharuddan kasar domin a dage dakatarwar.
Keyamo, wanda kuma mamba ne a kwamitin da aka kafa domin tattaunawa da Twitter a kan dakatar da shi, ya ce:
"Dalilin da ya sa shugaban kasar ya dauki wannan mataki shi ne don sake daidaita dangantakarmu da Twitter ba wai don korarsu daga kasarmu ba.
"Wannan sake fasalin, mun fara shi kuma shugaban ya saka ni a cikin kwamitin."
A baya kadan ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa, gwamnati za ta dage dakatarwar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wani masanin tsara kudi, Kalu Aja, ya ce:
"Haramcin Twitter ya ba da labari game da yin kasuwanci a Najeriya, kuma ba labari ba ne mai kyau.
"Musamman, Twitter da kafofin watsa labarun suna ba da dama ga Kananan Kamfanoni da Matsakaita da masu mallakarsu su yi talla ba tare da kasafin kudi na tallace-tallace ba face amfani da wayar hannu don ginawa da sadarda alkawarin kasuwanci."
Batun dakatar da Twitter
Idan baku manta ba, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumunta na Twitter a Nigeria kamar yadda gwamnatin ta sanar a shafin ma'aikatar Labarai da al'adu a Twitter.
Ministan sadarwa da al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da dakatarwa a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa ana amfani da shafin wurin aikata abubuwa da ke barazana ga hadin kan Nigeria.
Ministan ya kuma ce gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai, NBC, ta fara aikin bada lasisi ga dukkan dandalin sada zumunta ake amfani da su a kasar.
Asali: Legit.ng