Tsohon Gwamna ya baiwa kungiyar CAN buhun Shinkafa 400, Shanu 20, don murnar Kirismeti

Tsohon Gwamna ya baiwa kungiyar CAN buhun Shinkafa 400, Shanu 20, don murnar Kirismeti

  • Tsohon Gwamna AbdulAziz Yari ya yiwa mabiya addinin Kirista kyautar daruruwan buhun Shinkafa a jiharsa
  • Hakazalika al'ummar Igbo da Yarbawa dake jihar sun samu nasu kason na Shinkafa da Shanu
  • Hadiman gwamnan sun bayyana cewa Gwamnan tun yana mulki yana irin wannan kyauta shekara-shekara

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bada kyautan buhunan Shinkafa 400, Shanu 20, da Milyan daya ga kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, domin murnar Kirismeti.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kakakin tsagin Yari na jam'iyyar APC, Ibrahim Birnin Magaji, ya saki.

A cewarsa, bayan Kiristoci, Sanata Yari ya baiwa al'ummar Yarbawa da Igbo irin wannan kyautar.

Tsohon Gwamna Yari
Tsohon Gwamna ya baiwa kungiyar CAN buhun Shinkafa 400, Shanu 20, don murnar Kirismeti Hoto: Presidency
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin yace Yari ya samu wakilcin Sakataren Jam'iyyar, Sani Musa Talata Mafara, yace Tsohon Gwamnan ya dade yana irin wannan kyauta tun yana mulki.

Kara karanta wannan

Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

A cewar jawabin:

"A taron, Shugaban CAN ya karbi buhun Shinkafa 400, Shanu 10, da milyan 1. Kungiyar Inyamurai sun samu buhun Shinkafa 40, da Shanu 2. Yarbawa yan APC sun samu buhun Shinkafa 20, da Saniya guda yayinda APC Igbo suka samu buhun Shinkafa 40 da Shanu 2."
"Shugaban CAN, Rabaran Iliya Tsiga...ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar bisa kyautar da ya saba yi."

Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Gusau, ta yi fatali da karar da tsofaffin ciyamomin APC 10 dake goyon bayan tsohon gwamna, Abdul'azizi Yari suka shigar gabanta.

Channels tv ta rahoto cewa wani Abdul-aziz Danmaliki da wasu mutum 9 ne suka shigar da karar a watan Yuli, suna kalubalantar matakin APC ta ƙasa.

Masu shigar da karar sun kalubalanci matakin kwamitin rikon kwarya na APC karkashin gwamna Mai Mala Buni, na rushe shugabannin APC a Zamfara bayan sauya shekar gwamna Matawalle.

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng