An kama gungun matasa 11 da suka yi garkuwa da 'yan uwan sarki da jami'in kwastam, kuma suka kashe dan sanda

An kama gungun matasa 11 da suka yi garkuwa da 'yan uwan sarki da jami'in kwastam, kuma suka kashe dan sanda

  • Rundunar ‘yan sandan sirri ta jihar Taraba ta samu nasarar kama wasu matasa 11 bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane
  • Ana zargin su ne suka halaka sajan Ogidi Habu, sannan su ka yi garkuwa da jami’an kwastom tare da dan’uwan sarkin Jalingo
  • An samu nasarar kwace miyagun makamai daga hannunsu, kamar bindiga kirar AK47, kananun bindigogi tare da miyagun kwayoyi

Jihar Taraba - Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta samu nasarar kama wata kungiyar matasa 11 da ake zarginsu da harkar garkuwa da mutane, The Punch ta ruwaito.

Ana zargin mambobin kungiyar da halaka wani sajan din ‘yan sanda, Ogidi Habu a Jalingo tare da garkuwa da jami’in kwastom da dan’uwan sarkin Jalingo.

Yan sanda sun kama gungun miyagu da suka kashe dan sanda, sace jami'in kwastam da dan uwan sarki
An kama wadanda suka yi garkuwa da jami'in kwastam da dan uwan sarki. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

Wadanda ake zargin kamar yadda The Punch ta rahoto sun hada da Luka Adam, Shuaibu Nuhu, Moses Amos, Peters Mashi, Ahmadu Mallam, Adamu Mohammed, Dahiru Dalha, Gambo Isah, Sunusi Ahmadu, Mallam Mauludu da Ibrahim Idi, wadanda duk haifaffun jihar Taraba ne.

Har miyagun makamai aka amshe daga hannunsu

An samu nasarar amshe bindigogi bakwai (7) kirar AK-47, kananun bindigogi guda biyu, magazin hudu, takunkumin fuska, miyagun kwayoyi da sauran miyagun abubuwa daga hannunsu yayin da aka bisu har maboyarsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Frank Mba ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi ta wata takarda da ya saki mai taken, ‘Yan sanda sun kawo garanbawul akan sabon salon garkuwa da mutane a garin Taraba, sun kama masu garkuwa da mutane 11, sannan sun amshe bindigogi kirar AK-47 daga hannunsu.’

A cewarsa binciken ‘yan sanda ne ya bayyana wadanda ake zargin kuma dama rundunar ‘yan sanda ta dade tana nemansu ido rufe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Ya ce su na da alaka da sabon salon garkuwa da mutanen da ya fara aukuwa a jihar, har da kai wa jami’an tsaro farmaki.

An gano jagororin garkuwa da mutanen

Ya kara da cewa binciken ya nuna yadda Isah da Ahmadu ne jagororin halaka sajan din bayan barin sifetan ‘yan sanda da miyagun raunuka tare da satar jama’a a Jalingo.

Mba ya ce:

“Bincike ya kara bankado yadda ‘yan ta’addan su ke bin bayan ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da masu manyan motoci har gidajensu daga nan su shirya dabarar yin garkuwa da su.
“Su na amsar makudan kudade daga hannun ‘yan uwa da abokan arzikin mutane kafin su sake su. Yayin bincike, ‘yan sanda sun gano maboyarsu inda su ke boye jama’a idan sun sace su.
“An samu nasarar kwatar miyagun makamai daga maboyarsu sannan an saki wadanda su ka kama ba tare da an cutar da su ba, kuma tuni aka sada su da ‘yan uwansu. Yanzu haka ana ci gaba da bincike don gano wasu masu garkuwa da mutanen.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga

‘Yan sandan sun tabbatar da cewa za a gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu ana kammala binciken.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Kara karanta wannan

Hoton magidanci da ya jagoranci garkuwa da matarsa tare da halaka ta don ya gaji dukiyarta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164