Labari da Dumi-Dumi: Jami'an yan sanda sun damke Sarki a Najeriya
- Jami'an rundunar yan sanda sun kama wani sarki a jihar Delta bisa zarginsa kan badakalar filaye a yankinsa
- Mutanen yankin musamman matasa sun shiga tashin hankali, yayin da suka fara yaɗa cewa wasu ne suka yi garkuwa da sarkin su
- Hukumar yan sanda ta fito ta musanta rahoton sace sarkin, tace yana hannun jami'an FCID
Delta - Basaraken gargajiya na masarautar Okpanam, Sarkin Okpanam, HRM Michael Mbanefo Ogbolu, ya shiga komar yan sanda bisa zargin badaƙalar filaye.
The Nation ta ruwaito cewa, mutanen masarautarsa sun shiga tashin hankali a faɗin yankin bayan wasu jami'ai da ba'a gane ba sun zo sun yi awon gaba da shi.
Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa bayan haka, mutane sun fara yaɗa jita-jitar cewa wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa da shi.
Sai dai hukumar yan sandan reshen jihar Delta ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa an yi garkuwa da basaraken.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, shine ya musanta jita-jitar yayin da yake ƙarin haske kan kame sarkin.
Meyasa yan sanda suka kama sarkin?
Ya ƙara da cewa jami'an rundunar yan sanda na sashin binciken aikata manyan laifuka (FCID) su ne suka kama basaraken bisa zargin badaƙalar filaye.
A jawabinsa, kakakin yan sandan yace:
"Dan Allah, ina rokon ku Dan Allah, sarki da kuke ta yaɗa maganganu a kansa ba sace shi a ka yi ba, amma ya shiga hannun jami'an yan sanda na sashin binciken aikata manyan laifuka FCID."
Sai dai ya ƙara da cewa jami'an FCID ne kawai zasu iya bayyana dalilin da yasa suka kama basaraken.
Ko ya mutanen yankin suka ji?
Kama sarkin ya haifar da tashin hankali a yankin, yayin da matasa suka fito kan tituna suna mai bayyana lamarin da abu mai muni.
Matasan sun bayyana cewa wasu mutane a motar Sienna ne suka yi awon gaba da sarkin a kan hanyar dawowa daga coci.
Tribune Online ta rahoto cewa matasan sun roki mutane su kulle shagunan su har sai an gano inda sarkin su yake.
A wani labarin na daban kuma Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle
Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya.
Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda.
Asali: Legit.ng