Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

  • Sarkin kasar Zonkwa, Mai martaba Nuhu Bature ya rasu a ranar Asabar 18 ga watan Disamba, 2021
  • Nuhu Bature shi ne Sarki na farko da gwamnatin Jafaru Isa ta nada bayan kafa masarautar Zonkwa
  • Gwamna Nasir El-Rufai da Muhammadu Buhari sun fitar da sakon ta’aziyya ga mutanen Kaduna

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi wa mutanen kasar Zonkwa da iyalan Mai martaba ta’aziyyar rasuwar Agwam Kajju, Malam Nuhu Bature.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021, cewa Malam Nasir El-Rufai ya aika sakon ta’aziyyar rashin Sarkin Zonkwa, Nuhu Bature.

Gwamna Nasir El-Rufai yace Marigayi Sarkin Zonkwa mutumin kirki ne kuma Basarake na kwarai wanda ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Rahoton yace gwamnan ya yabi irin shawarwarin da Nuhu Bature ya bada a lokacin yana raye.

Kara karanta wannan

Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna

Jawabi daga bakin Muyiwa Adekeye

Mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna wajen harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya fitar da sakon ta’aziyyar a yammacin ranar Lahadi.

Basarake ya mutu a Kaduna
Buhari a garin Kaduna Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

“Gwamnatin jihar Kaduna ta na yabo da jinjinawa matsayinsa na uban kasa wanda ya hada-kan jama’a domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
“Malam El-Rufai ya aiko da sakon ta’ziyyarsa ga iyalin marigayi Sarki, ya na rokon Ubangiji ya sa ya huta, ya ba danginsa da daukacin kasar Zonkowa hakuri.”

- Muyiwa Adekeye

Masarautar kasar Zonkwa

Tun a shekarar 1995, Malam Nuhu Bature ya zama Agwam Bajju watau Sarkin kasar Zonkwa, a larimar hukumar Zangon-Kataf, ya yi shekara 21 a kan sarauta.

A 1995 gwamnatin Kanal Lawal Jafaru Isa ta kafa masarautar Zonkwa da Atyap a sakamakon mummunan rikicin da ya barke a Zangon-Kataf, aka rasa rayuka.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Buhari ya aiko da sakon ta'aziyya

Haka zalika Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ta’aziyyarsa ga gwamnatin Kaduna da mutanen kasar Zonkwa a kan rashin Marigayi Bature.

Gwamnoni za su fito da sabon littafi

A makon jiya ne aka ji Gwamnonin jihohi za su buga littafi kan yadda za a magance matsalar kasar nan. Kowane gwamna zai bada gudumuwarsa a rubutun.

Shugaban kungiyar NGF, Kayode Fayemi ya bayyana cewa wadanda za su zama Gwamna nan gaba, za su amfana da shawarwarin Gwamnonin na yau a littafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng