Lawan ya jagoranci sanatoci zuwa Daura wurin nadin sarautar Yusuf Buhari
- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya dira a garin Katsina domin garzayawa Daura wurin nadin sarautar Yusuf Buhari
- A safiyar Asabar, Lawan ya sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'Adua inda Gwamna Aminu Bello Masari ya karba Lawan da wasu sanatoci
- Sanata Bello Mandiya, Yusuf Abubakar Yusuf, Mohammed Sani Musa, su ne sanatocin da Lawan ya jagoranta domin halartar nadin sarautar
Daura, Katsina - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya isa Katsina a safiyar Asabar domin halartar nadin sarautar Yusuf, da daya tilo namiji da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mallaka.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya karbe su bayan sun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'Adua da ke Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, zai nada Yusuf sarautar Talban Daura, hakan zai sa ya zama hakimin Kwasarawa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, za a yi shagalin bikin nadin sarautar ne a Daura, asalin garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A tare da shugaban majalisar dattawan daga Abuja, akwai sanata Yusuf Abubakar Yusuf, Mohammed Sani Musa da Bello Mandiya.
Shugaban majalisar ana tsammanin zai koma Abuja bayan kammala nadin sarautar.
Shugaban kasan a halin yanzu ya na kasar Turkiyya tare da uwargidansa domin halartar wani taro.
Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki
A wani labari na daban, da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.
Ya ce: "Ko da baka kaunar Buhari, kan san cewa Daura a yanzu ta banbanta da yadda ta ke shekaru shida da suka gabata. Don haka, mun masa tukwici kan karamcin da ya yi mana, mun bawa dansa daya tak, Yusuf, sarautar Talban Daura. Hakan zai hana shi yawo zuwa Yola (garin mahaifiyarsa) da Abuja.
"Daga Jami'ar Fasahar Zirga-Zirga zuwa Kwallejin Fasaha ta Tarayya, ga tituna da wasu manyan ayyukan raya kasa da cigaba. A yau, Daura ta fi wasu jihohin Najeriya a bangaren cigaba."
Asali: Legit.ng