Da duminsa: Canada ta dage takunkumin hana shigar 'yan Najeriya kasar
- Kasar Canada ta dage takunkumin da ta saka wa Najeriya da wasu kasashen Afrika goma na hana su shiga kasar
- Ministan lafiyan kasar, Jean-Yves Duclos, ya sanar da wannan hukuncin yayin jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a
- Canada ta saka wannan takunkumin ne domin gujewa isar kwayar cutar korona nau'in Omicron zuwa kasar
Canada - Gwamnatin kasar Canada ta dage takunkumin da ta saka na haramta wa jama'ar kasashe goma na Afrika da suka hada da Najeriya shiga kasar.
TheCable ta ruwaito cewa, Jean-Yves Duclos, ministan lafiya na kasar Canada, ya sanar da wannan hukunci a wani jawabi da yayi wa manema labari a ranar Juma'a.
Wannan cigaban ya na zuwa ne bayan makonni uku da gwamnatin kasar Canada ta haramta wa kasashe goma da suka hada da Najeriya daga shiga kasar kan tsoron yada sabon nau'in cutar korona na Omicron.
Sokoto: Tambuwal ya ɗauki mataki kan mawaƙin da ya gwangwaje shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, da waƙar yabo
Baya da Najeriya, sauran kasashen da lamarin ya shafa ya hada da Botswana, Egypt, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, South Africa da Zimbabwe, The Cable ta ruwaito hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yayin jawabi kan janye takunkumin, ministan ya ce sabon cigaban zai fara aiki ne daga ranar 18 ga watan Disamba.
"A yayin da muka fuskanci wannan lamarin ya dauka wani salo, mun yarda cewa ya zama dole mu dauka mataki wurin dakile isowar cutar korona nau'in Omicron a Canada," Duclos yace.
"Ganin halin da ake ciki, wannan matakin ya yi amfanin shi kuma yanzu babu bukatar shi."
Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona
A wani labari na daban, kasar Kanada ta sanya dokar hana shigar yan Najeriya kasar a wani yunkuri na dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron, Daily Trust ta ruwaito.
Kasar ta Arewacin Amurka da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan ne a safiyar yau Laraba 1 ga watan Disamba.
Ya zuwa yanzu, hukumomin Kanada sun haramtawa kasashe 10 shiga kasarsu saboda bullar sabon nau'in na Korona.
Kasashen sun hada da Afirka ta Kudu da Namibiya da Lesotho da Botswana da Eswatini da Zimbabwe da Mozambique da Najeriya da Malawi da Masar.
Ministan Sufuri na Kanada Omar Alghabra, ya ce ‘yan kasashen waje da suka je wadannan kasashe a cikin kwanaki 14 da suka gabata za a hana su shiga kanada na wani dan lokaci.
Asali: Legit.ng