Da Dumi-Dumi: Tsohon Minista a Najeriya, Alhaji Hussaini, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Labarin da muke smau daga jihar Nasarawa ya nuna cewa tsohon ministan Kwadugo, Alhaji Hussaini Zanwa, ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayin, wanda ya rike mukamin minista a shekarar 2003, ya rasu ne ranar Jumu'a bayan fama da rashin lafiya
- Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, yace tuni aka gudanar da jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ta tanada
Nasarawa - Tsohon ministan gwadugo da kirkire-kirkire, Alhaji Hussaini Zanwa Akwanga, ya riga mu gidan gaskiya.
Akwanga, ya rasu ranar Jumu'a, yana da shekaru 77 a duniya bayan fama da dogon rashin lafiya a mahaifarsa, Akwanga, hedkwatar karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa.
Vanguard ta ruwaito cewa tsohon ministan, wanda kwararre ne a harkar koyarwa, ya zama minista ne a shekarar 2003.

Source: UGC
Sai dai marigayin ba'a kammala wa'adin mulki da shi ba, inda tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya sallame shi daga bakin aiki.
A shekarar 2017, wasu yan bindiga suka sace tsohon ministan a gonarsa dake ƙauyen Kurmin Tagwaye, kusa da garin Akwanga, amma ya kuɓuta kwana biyu da sace shi, bayan an biya kudin fansa.
Hukumomi sun tabbatar da rasuwarsa
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akwanga dake jihar Nasarawa, Alhaji Safiyanu Isa, ya tabbatar da rasuwar tsohon ministan.
Yace:
"Tsohon ministan ya rasu ne yau Jumu'a 17 ga watan Disamba, 2021 a garin Akwanga, karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa."
Kazalika mataimakin shugaban ya tabbatar da cewa tuni aka gudanar jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanazar mahaifarsa, Akwanga.
A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023

Kara karanta wannan
Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano
Gabanin zaɓen gwamnan jihar Kaduna dake tafe a 2023, tsohon gwamna, Mukhtar Ramalan Yero, yace zai sake neman ɗarewankujerar gwamna.
Vanguard ta ruwaito Yero na cewa a halin yanzun al'ummar Kaduna sun gane banbancin dake tsakanin jam'iyyar PDP da kuma APC.
Asali: Legit.ng
