Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano

Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano

  • Kotun tarayya sake tabbatar da shugabannin jam'iyyar APC na Kano tsagin Sanata Ibrahim Shekarau
  • Kotun ta jadadda cewa tsagin Sanata Ibrahim Shekarau da suka zabi Harun Zago a matsayin shugabansu na halatattun shugabanni
  • Kotu ta ce tsagin na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba su yi zabuka a matakin mazaba da kananan hukumomi

Wata babbar kotun tarayya dak zamanta a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Sharia Hamza Muazu ta tabbatar da tsagin Shekarau ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC a Kano.

Yayin Shari'a ranar Juma'a, Alkalin ya yi watsi da karar tsagin Ganduje kuma ya ci su tarar milyan daya kan batawa kotu lokaci, rahoton DailyNigerian.

Kotu ta tabbatar da cewa zaben da tsagin Shekarau tayi shine daidai kuma shugabanninsu ne shugabannin APC a jihar.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotu: Ku kwantar da hankulanku, Ganduje ya yi kira ga mabiyansa

Abdullahi Abbas ne ke jagorantar tsagin Ganduje yayin da Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar tsagin Shekarau.

Rikicin APC a Kano
Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya zaku tuna cewa a ranar 30 ga Nuwamba, kotu ta soke dukkan shugabannin jam'iyyar All Nigeria Peoples Congress da ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Alkalin Ya ce tsagin Gwamna Ganduje ba su yi zabe a matakin mazabu ba da kananan hukumomi.

Amma tsagin Ganduje basu amince da hakan ba inda suka koma kotu ta dakatad da wanzar da hukuncin da tayi.

Sai yanzu kotun ta zauna kuma ta yanke hukunci.

Sanatoci 2, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje

Sanatoci biyu dake wakilatar jihar Kano da wasu yan majalisar dokokin tarayya sun hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Kano dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya

An bayyana cewa yan majalisun sun hadu ne domin kwace mulkin jam'iyyar APC hannun gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje yayinda ake shirin zaben shugabannin jam'iyyar

Sanatocin sun hada da Ibrahim Shekarau (APC-Kano ta tsakiya) da Barau Jibrin (APC-Kano ta Arewa)

Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sha’aban Sharada (APC-Kano Municipal), Tijjani Jobe (APC-Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado); Haruna Dederi (APC-Karaye/Rogo) and; Nasiru Auduwa (APC-Gabasawa/Gezawa).

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng