Kungiya Ta Yi Kira Ga 'Yan Kudancin Najeriya Su Saka Baki Don Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe a Arewa
- An bukaci mazauna kudancin Najeriya su taya mutanen arewa zanga-zanga da suke yi na nuna rashin amincewa da hare-haren 'yan bindiga da ta'addanci
- Wasu kungiyoyin arewa sun fara zanga-zanga ta #NorthIsBleeding da #SecureNorth don janyo hankali kan hare-haren da 'yan ta'adda ke yi a yankin
- Wata kungiyar kare hakkin bil adama ta bukaci yan kudancin Najeriya su shiga a yi da su domin yan ta'addan suna iya karasawa kudu bayan sun gama da arewa
FCT, Abuja - Wata kungiyar kare hakkin bil adama, Take it Back Movement ta yi kira ga 'yan Najeriya daga yankin kudu su taya yan uwansu na arewa janyo hankalin gwamnati kan kashe-kashen da ake yi a yankin.
Wani sashi na sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Adeolu Steve, ya fitar a ranar Talata 14 ga watan Disamba, kamar yadda SaharaReporters, ya ce:
"Idan muka bari 'yan ta'adda suka mamaye arewa, kuna ganin mutanen kudu za su zauna lafiya? Abin da ya fi dacewa shine duk mu tashi tsaye, mu manta da banbancin da ke tsakanin mu, muyi fada a matsayin tsintsiya madaurin ki daya!"
"Ana ta cigaba da kashe-kashe ne a arewa saboda mun saki jiki. Ya kamata mu farka daga barcinmu sannan mu fuskanci barazanar da ke tunkarar mu.
"Domin samar da tsaro a arewa, muna bukatar jagoranci da zai hada kan dukkan mu wuri daya kowa ya bada gudunmawa."
Kano: Bayan Amsa Gayyatar SSS, Ɗaya Cikin Wadanda Suka Shirya Zanga-Zanga Ta Ce Ta Tsamme Hannunta
A baya, kun ji cewa daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar #NoMoreBloodshed a Kano, Zainab Naseer Ahmed, ta ce ta tsame hannun ta daga zanga-zangar, jim kadan bayan fitowa daga ofishin yan sandan farin kaya, SSS.
Tunda farko SSS ta gayyaci Zainab ne domin amsa tambayoyi kan rawar da ta taka wurin shirya zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin arewa da Abuja don janyo hankalin gwamnati kan rashin tsaro a arewa bayan kisar gillar da aka yi wa matafiya 42 a Sokoto.
Bayan shafe kimanin awa biyu a ofishin SSS, Zainab Ahmad ta wallafa a shafinta na Facebook cewa daga yanzu ta tsame hannun ta daga zanga-zangar.
Asali: Legit.ng